ASIRIN MUHYI MAGAJI YA TONU!!!
Allura na neman Tono Garma inda Munafurcin Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado ya Bayyana - Haruna Abubakar Bebeji Gabatarwa : Maido da Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin shugaban Hukumar Karɓan Ƙorafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano a kwanan nan ya sanya wasu daga cikin al'umar Jihar Kano fatan samun adalci da gaskiya a jihar. Amma wasu batutuwa da suka fara bayyana a baya-bayan nan sun sanya ayar tambaya akan nagarta da gaskiyar sabon shugaban Hukumar ta PCACC. Ya bayyana cewa ayyukan Rusau da ake yi da sunan maido da martaba, tarihi da al'adun Jihar Kano ba komai ba ne face bita da ƙulli irin ta siyasa da ake yi wa gwamnatin da ta gabata ta Gwamna Ganduje. Yayin da Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Muhyi kan muƙamin sa don ƙarasa wa'adinsa, abinda ya aikata sun sa al'uma sun fara kokwanto a kansa da kuma hukumarsa inda hankalin jama'a ya karkata zuwa garesu. Muh...