SHIRIN TATTAUNAWAR ƊAKIN GABON NA ƘARA KAMA ZUCIYAR MASU KALLO
Ƙayataccen Shirin Gabon's Room Talk Show: Dole a Yaba da Ƙoƙarin Mai Gabatar da Shirin da Mara Mata Baya - Haruna Abubakar Bebeji
Gabatarwa:
A fagen shirye-shiryen tattaunawa, duniyar Hausawa ta samu cigaba da tagomashi da wani shiri da ya fito da yake jan hankalin masu kallo a duk yammacin ranar Alhamis. Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, ta ɗauki wani sabon salo a matsayin mai gabatar da shirin nan mai matukar farin jini na tattaunawa da baƙi, da tayi wa laƙabi da Gabon's Room Talk Show (Tattaunawar Ɗakin Gabon). A kowane mako, Gabon ta kan gayyato fitattun jaruman Kannywood da kuma wasu fitattun mutane a wasu ɓangarorin, inda ta samar da wani dandali na nishaɗantarwa, inda ake tattauna batutuwa masu zurfi, tare da fito da sirrukan shahararrun mutane dake ɓoye daga bakunan su.
Shirin Gabon's Room Talk Show ya ƙarawa masana'antar Kannywood ƙima da wani sabon salon nishaɗi a Arewacin Najeriya. Shirin da ke kara samun karɓuwa a kowane mako, wani yunƙuri ne mai ƙarfi na sauya labarin koma bayan da Kannywood ta yi a shirye-shiryen talabijin da kuma shirye-shiryen tattaunawa musamman hirarraki da fitattun jaruman masana'antar.
Duk da cewa ba ta da shaidar ƙwarewar aikin jarida, shirin tattaunawa na Hadiza Gabon na ƙara samun farin jini saboda yadda take hira da fitattun jaruman Kannywood. Shirin dai ya ƙunshi tattaunawa da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da mashahuran mutane kama daga ƴan siyasa da ƙwararru a fannoni daban-daban. Shirin ya kuma ƙunshi tattaunawa da manyan ƴan Najeriya da suka haɗa da manyan ƴan siyasar kasar, ƴan kasuwa, fitattun mutane, da dai sauransu.
Nishaɗi Mai Ƙayatarwa:
Shirin Tattaunawa na Ɗakin Gabon ya fara jan hankalin al'uma ne tun daga shirye-shiryen sa na farko, inda Gabon ba tare da shayi ba, ba ta yiwa shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Rakiya Moussa Poussi ƴar asalin Ƙasar Nijar tambayar ƙwaƙwaf game da rayuwar soyayyarta. Ta hanyar tambayoyin ƙwaƙwaf ɗin da take yi, shirin na Gabon ya fara mamaye zuƙatan miliyoyin mutane yayin da Rakiya ta bayyana irin soyayyar da ta ke yiwa wani fitaccen mawaƙin Hausa, wanda shi kuma baya gani ko ɗaukar soyayyar tata da muhimmanci. A wannan hirar, shirin ya fara janyo hankulan ƴan kallo daga ko ina tare da burgesu nan take.
Samar da Shirin na Gabon's Room Talk Show a masana'antar Kannywood abin farin ciki ne, wanda zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin masana'antar zuwa wani sabon mataki. Shirin wanda yake baje kolin ɗumbin hazaƙa da ƙwazon Mashahuran ƴan Arewa, yana ba da wani dandamali ne ga jaruman masana'antar ta Kannywood da wasu ƴan Arewa da Allah ya ɗaukaka su a duniya.
Irin Manyan Baƙin da suka Halarci Shirin waɗanda ba za a iya mantawa da su ba
A kowane Mako, Shirin Tattaunawar Gabon's Room Talk Show na ci gaba da nishaɗantar da masu kallo tare da jerin manyan baƙi daga masana'antar Kannywood da wasu ɓangarori. Fitattun jaruman Kannywood irin su Ali Nuhu, Sani Danja, Adam A. Zango, Alan Waka, da Fati Mohammed da sauran su duk sun halarci shirin, inda suka ba da haske da kuma bayanan sirri da suke burge mabiya da masoyan su.
Fitar da batutuwan da masu kallo basa tsammanin jin su, Gabon ta faɗaɗa tunanin tunanin shirin ta hanyar gayyatar fitattun mutane daga sassa daban daban bayan masana'antar nishaɗi ta Kannywood. Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, mai rajin kare haƙƙin bil'adama Nastura Ashir Sharif, da fitaccen ɗan siyasar nan Sani Sha'aban duk sun fito a cikin shirin, inda suka ƙara ƙayatar da shirin da fito da bayanai na irin gwagwarmayar da suka yi a rayuwar su.
Amfani da Manhajar YouTube wajen Watsa Shirnta:
Ta kafar tasharta ta YouTube mai suna "Hadiza Aliyu Gabon," mai gabatar da shirin tana tabbatar da cewa masoya na kusa da na nesa suke samun damar kallon shiri. Ta hanyar fitar da sabon shiri kowane ranar alhamis da yamma, Gabon tana ƙoƙarin ganin masoya shirin suna marari da dakon fitar da sabon shirin ta don nishaɗantar su, ƙara musu ilimi, da zabura da su.
Babbar Muhawara da ake yi: Ƙwarewa da Shuhura:
Wasu masu sukan shirin dai na cewa rashin ƙwarewar da mai gabatar da shirin Hadiza Gabon a aikin jarida na kawo cikas ga ingancin shirin. Sai dai kuma shuhurarta da ɗaukakar ta a masana’antar Kannywood ne ke baiwa Gabon ɗin damar samun sabbin labaran dake ɓoye da kuma tattaunawa batutuwa na gaskiya daga bakin jaruman dake halartar shirin ta. Ƙoƙarin ta na amfani da alaƙa na kusa da take da shi da abokan sana'ar ta, shi ke bata dama na samar da irin waɗannan ɓoyayyun bayanai daga wajen su, wanda hakan ne yasa shirin ke ƙara samun karɓuwa da masu bibiyar shirin.
Haƙiƙa wannan Shirin Tattaunawa tayi matukar tasiri ga harkar nishaɗantarwa a Arewacin Najeriya. Ya nuna cewa ƴan masana'antar Kannywood suna da wasu basirar da basu taƙaita kawai a fitowa a matsayin jarumai ko masu taka rawa kawai a cikin wasannin kwaikwayo ba; lallai suna ƙoƙarin ɓulle da wasu sabbin salo da ɗaukaka masana'antar zuwa mataki na gaba. Har ila yau, ya nuna sauye-sauyen da ake samu wajen fito da basirar dake malale a Arewacin Najeriya, tunanin da a baya ake tunanin bamu da masu basira a Arewa.
Duk da yake akwai buƙatar inganta shirin a salon irin tambayoyin da Hadiza Gabon ke yiwa baƙin ta, amma babu wanda zai musa irin ƙayataccen nishaɗin da shirin na Gabon's Room Talk Show ya samar. Shiri ne mai nishaɗantarwa, faɗakarwa, da barin masu kallo da buƙatar kawo Babban Baƙo ko Baƙuwa na gaba. A matsayinmu na masu bibiyar shirin, da wasu ƙayatun shirye-shirye masu inganci, ya zama wajibi mu ba da goyon bayanmu ga Gabon, tare da ƙarfafa mata gwiwa ta inganta shirin nata domin ya kasance mafi kyau da ƙara ƙwarewa a fagenta.
Dole ne a yabawa wannan shirin na tattaunawa na Gabon's Room Talk Show bisa yadda yake nuna yadda masana’antar nishaɗantarwa ta Arewacin Najeriya yake ga al'umar duniya. Shirin ya samar da wata kafa ga jarumai da wasu ƙwararru a fannoni daban daban wajen ɗaga darajar yankin mu da al'adun mu ta hanyar hira da mutane daban-daban a yankin. Muhawarar da ake yi a shirin da kuma bayanai masu ban sha'awa sun sanya ya zama shiri da kowa ke son kallo kuma abin sha'awa ga masu kallo ba wai a Arewacin Najeriya kaɗai ba har ma da sauran sassan duniya.
Rufewa:
Gabon's Room Talk Show has emerged as a force to be reckoned with in the talk show genre. Hadiza Aliyu Gabon's ability to fuse entertainment and personal connections gives the show a profound appeal.
Shirin Tattaunawa na Gabon's Room Talk Show ya fito a matsayin wani sabon shiri da zai goga kafaɗa a cikin nau'in irin shirye-shiryen tattaunawa. Ƙo Hadiza Aliyu Gabon wajen haɗa nishaɗi da alaƙarta da abokan aikin ta, ya taimaka wajen bawa shirin tagomashi da jan hankalin masu kallo sosai.
Ya zama wajibi mu a yabawa shirin Tattaunawa na Gabon's Room Talk Show, bisa namijin ƙoƙarin da shirin ke yi na farfaɗo da masana’antar Kannywood da ɗaga darajar Arewacin Najeriya a idon duniya, da nuna al’adun Arewa da kuma faɗaɗa kasuwar masana’antar ta hanyar zamani a ɓangaren yaɗa labarai da nishaɗantarwa.
Tare da goyon bayan ku, za mu iya taimaka wa Shirin Gabon ya zama fitila mai haskakawa ba kawai a tsakanin al'ummar Arewacin Najeriya ba har ma a tsakanin masu jin harshen Hausa a duk faɗin duniya. Mu haɗu wajen marawa shirin baya tare da rungumar irin salon farin ciki da nishaɗin da shirin ke kawowa a fuskokinmu a kowane mako.
Ina taya Hadiza Gabon murnar wannan yunƙuri nata; muna dakon cigaba da kallon shirye-shiryen da take tafe da su a nan gaba na Shirin Tattaunawar Ɗakin Gabon wato Gabon's Room Talk Show.
Sunana Haruna Abubakar Bebeji.
Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya. Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su.
Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci. Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.
A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina.
Na gode da ziyartar shafina.
Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.
Comments
Post a Comment