DAGA FADAR SHUGABAN ƘASA
ZAMU MAGANCE MATSALAR DAKE TATTARE DA ƊAUKAR NAUYIN TSARIN KULA DA LAFIYA A MATAKIN FARKO - Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima
Gidauniyar Gates Za Ta Kashe Dala Biliyan 7 Akan Matsalolin Ɗaukar Nauyin Kula da Lafiya a Matakin Farko Nan Da Shekaru Hudu Masu Zuwa
Za mu magance matsalolin da ke tattare da samar da kuɗaɗe na tsarin kiwon lafiya a matakin farko a ƙasar nan, in ji mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima.
Mataimakin shugaban ƙasan wanda ya bayyana cewa cutar shan inna na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen kiwon lafiya a matakin farko a ƙasar nan ya bayyana cewa “shawarar ita ce samar da kuɗaɗe daga cikin ƙasar kan lokaci don samar alluran rigakafin, wanda ba zasu iya samuwa da wuri ba, don bunƙasa masana’antunmu na cikin gida don samar da rigakafin."
Mataimakin Shugaban Ƙasan ya bayyana haka ne a yau a wani taro da wasu Gwamnoni a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya suka yi da Alhaji Aliko Dangote da Bill Gates a ɗakin taro na Banquet Hall dake fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.
Yayin da yake tabbatar da barazanar da Najeriya ke fuskanta a fannin cutar shan inna, ya bayyana cigaban da aka samu na cewa wadatuwar allurar rigakafin cutar shan inna a Najeriya ya ƙaru daga kashi 33% a shekarar 2016 zuwa kashi 57% a shekarar 2021.
Ya ci gaba da cewa, “Bambancin ƙwayar cutar shan inna ta ragu a Najeriya da kashi 84% daga shekarar 2021, inda ta faɗi ƙasa zuwa yara 200 na masu kamuwa da cutar a shekarar 2022. Don haka ya yabawa jihohin da suka samu cikakkiyar damar samar da rigakafin, wanda ke tsakanin kashi 60% zuwa 80% na alƙaluman wuraren da suka ƙuduri aniyar yin rigakafin, inda kuma adadin jihohin ya ƙaru daga Jihohi 12 zuwa 21 a cikin shekaru biyar."
Da yake ba da ƙarin tabbacin, ya ce, “Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin mu za su samar da kyakkyawan tsari da sabbin hanyoyi da dabaru na kankare tarihin ƙasar nan jerin ƙasashe dake kan gaba masu yawan jarirai da ba a yi wa rigakafi ba a duniya a cikin shekaru goma da suka gabata."
Mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya jaddada cewa, "gwamnatin tarayya ta himmatu wajen kawar da na'ukan cutar shan inna, nan da ƙarshen shekara, tare da tabbatar da cewa kowane yaro ɗan Najeriya yaci moriyar rigakafin yau da kullum.
Dangane da batun sarrafawa da samar da alluran rigakafin rigakafin yara, ya ba da tabbacin cewa, “za mu haɗa kai don ganin an samar da waɗannan alluran rigakafin wanda zai wadaci yaran dake buƙatar rigakafin, wanda adadin da muke da su sun kai miliyan 2, wanda sune adadi mafi girma a faɗin duniya bayan ƙasar Indiya."
Daga nan sai mataimakin Shugaban Ƙasan ya bayyana jin daɗin gwamnatin tarayya ga abokan hulɗa irin su gidauniyar Alhaji Aliko Dangote da gidauniyar Bill Gates, waɗanda yace tausayin su ya bayyana a wannan lokaci maras tabbas a tarihin mu.
Tun da farko a jawabinsa a wajen taron tattaunawar, babban Attajiri Bill Gates ya bayyana cewa, a baya-bayan nan gidauniyarsa ta bayyana aniyar ta na bayar da dala biliyan 7 ga Afirka nan da shekaru huɗu masu zuwa don tallafawa rigakafin yau da kullun a Najeriya, da shirin kawar da cutar shan inna daga doron ƙasa a Arewacin Najeriya.
Shi ma a nasa jawabin, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa Bill Gates da shi kansa sun shafe shekaru da dama suna aikin haɗin gwiwa da gwamnatocin tarayya da na Jihohi, tare da tallafawa ƙoƙarin da ake yi na kawar da cutar shan inna da inganta rigakafi na yau da kullum, samar da abinci mai gina jiki da kiwon lafiya a matakin farko a ƙasar nan.
“Mun yi amannar cewa Shawarwarin da Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa zata yanke nan da shekaru huɗu masu zuwa, su zasu tabbatar da ko Najeriya na da ingantaccen cigaban tattalin arziki, da samarwa ƴan Ƙasa farin ciki da kuma cimma burin muradun cigaba mai ɗorewa,” in ji shi.
A jawaban da suka yi daban daban, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Alhaji Abdulraman Abdulrasaq da wasu gwamnonin da suka yi jawabi a wurin taron sun yaba da yadda gidauniyar Dangote da Bill & Melinda Gates suke gudanar da ayyukan jin ƙai a fannonin da suka haɗa da kiwon lafiya, ilimi, noma da cigaban al'uma.
Gwamnonin sun bayyana shirin su na ƙara haɗa kai da gidauniyar Dangote da Gates a shekaru masu zuwa.
Olusola Abiola
Darektan Yaɗa Labarai,
Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa
Yuni 22, 2023
Comments
Post a Comment