ASIRIN MUHYI MAGAJI YA TONU!!!
Allura na neman Tono Garma inda Munafurcin Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado ya Bayyana - Haruna Abubakar Bebeji
Gabatarwa:
Maido da Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin shugaban Hukumar Karɓan Ƙorafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano a kwanan nan ya sanya wasu daga cikin al'umar Jihar Kano fatan samun adalci da gaskiya a jihar. Amma wasu batutuwa da suka fara bayyana a baya-bayan nan sun sanya ayar tambaya akan nagarta da gaskiyar sabon shugaban Hukumar ta PCACC. Ya bayyana cewa ayyukan Rusau da ake yi da sunan maido da martaba, tarihi da al'adun Jihar Kano ba komai ba ne face bita da ƙulli irin ta siyasa da ake yi wa gwamnatin da ta gabata ta Gwamna Ganduje.
Yayin da Gwamna Abba Yusuf ya mayar da Muhyi kan muƙamin sa don ƙarasa wa'adinsa, abinda ya aikata sun sa al'uma sun fara kokwanto a kansa da kuma hukumarsa inda hankalin jama'a ya karkata zuwa garesu. Muhyi da kansa ya tabbatar da cewa hukumar za ta gudanar da bincike a kan yadda aka raba filaye ba bisa ƙa'ida ba domin samun hujja ko kuma akasin haka, amma wannan sabon badaƙalar da ya kunno kai ya sanya shakku kan ko Muhyin zai iya gudanar da aikinsa ba tare da nuna son kai ba.
Wanda yaci Moriyar Haramtacciyar Fili Ya Juya Zuwa Mai Bincike:
Kwanan nan Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana a gidan Talabijin na Trust TV inda yake cewa hukumarsa za ta binciki waɗanda ake zargi da karkatar da filayen da ake rusuwa a faɗin jihar. Sai dai kuma ya bayyana cewa shi ma da kansa ya ci gajiyar irin wannan rabon da yake zargin an yi su ba bisa ƙa'ida ba. A wani al’amari mai ban mamaki, an gano cewa Muhyi ya sayar da filin nasa kan kuɗi Naira miliyan 15. Wannan badaƙala mai girma na son zuciya da munafurci na Muhyin ya fara haifar da shakku da tambayoyi game da gaskiya da amincin binciken hukumarsa.
Tonon Sililin da Rabon Filayen Gwamnati Ya Haifar:
Ɗaya daga cikin waɗanda suka sayi Filayen da aka ce an raba su ba bisa ƙa'ida ba, Alhaji Ismail Bello wanda shi ne sakataren Tsare-Tsaren Ƙungiyar BUK-Haure Property Owners Forum ya zo da wasu sabbin bayanai. Ya bayyana cewa Shima Muhyi Magaji ya rabauta da ɗaya daga cikin filayen wanda yake daura da ginin Ofishin Gidauniyar Jihar Kano da ke kan titin BUK, wanda a yanzu ya koma kamfanin sayar da motoci. Har ila yau, mutumin ya ƙara da cewa wasu fitattun mutane da suka haɗa da Marigayi Alhaji Bashir Tofa, Alhaji Wada Aliyu Gaya, Abdulaziz Ganduje, da sauran su, suma duk sun ci gajiyar samun irin waɗannan Filayen da aka ce an raba ba bisa ƙa'ida ba.
Har wa yau ɗaya daga cikin masu Filayen ya zargi Muhyi da munafurci da rashin adalci da yin ruwa da tsaki wajen rusa kadarorin da ake zargi an raba su ba bisa ƙa'ida ba, wanda shima ya amfana. A bayyane yake cewa furuci da irin zaƙewar Muhyi akan wannan lamari sun saɓawa ƙa'idojin adalci da rashin nuna son kai da ya kamata su zama ginshiƙan da suka kafa Hukumar Yaƙi da cin hanci da rashawa. Mutumin ya bayyana kaɗuwa da mamakin sa ta yadda Muhyi ya juya a baya-bayan nan ya zamo cikin masu zaƙewa da fito-na-fito da waɗanda suke da Filaye a wuraren waɗanda gwamnatin da ta gabata ta basu.
Fakewa da Dawo da Martaba da Asalin Tsarin Jihar Kano ta Hanyar Cin Zarafin Al'uma da Ramukon Gayya irin ta Siyasa:
Wannan aikin rusau da ake yi, wanda a cewar Gwamnatin Jiha ana yi ne bisa hujjar kare ababen tarihi da dawowa da tsarin Kano, sai dai a bayyane yake cewa Rusau ɗin na da nasaba da siyasa. Wasu fitattun mutane daga tsohuwar gwamnatocin da suka gabata wanda suka haɗa da Tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon Gwamna Ganduje, suma sun ci gajiyar irin waɗannan rabon filayen, amma duk da haka, ba a zana jan Fenti dake nuna alamun za a ruguje su ba. Ware irin waɗannan gine-gine su ke daɗa tabbatar da rashin adalci da haifar da zargi tare da sanya shakku na ainihin manufar Rusau ɗin.
Ƙarshe:
Bayyanar munafurcin Muhyi Magaji Rimin Gado ƙarara da rikiɗewar sa zuwa wani mutum mai fuska biyu ya fara kawo cikas ga kwarjini da mutuncin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano. Wannan aikin da da ake yi na Rusau, wanda gwamnati mai ci ta gabatar a matsayin wani gagarumin ƙoƙari na maido da kayayakin tarihi, an gano cewa ya rikiɗe zuwa ayyukan ɓarna saboda cimma wani buri na siyasa wani da ake so a muzanta tare da muzgunawa gwamnatin da ta shuɗe. Ya zama wajibi al'ummar Jihar Kano su buƙaci Shuwagabbani ko kuma jagorori suyi aiki da gaskiya, adalci da riƙon amana daga shugabanninsu domin kawar da matsalar cin hanci da rashawa a kowane fanni a faɗin Jiha.
Haka kuma ya zama wajibi Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta yi aiki da cikakken gaskiya da kyakkyawar mu'amala domin samun yardar al’umma da amincewar su. Asirin Muhyi da ya tonu ya sanya ayar tambaya kan sahihancin hukumar baki ɗaya, kuma dole ne a sake duba aikin Rusau da ake yi domin ganin ba a yi shi da wata manufa ta siyasa ba. Yana da matuƙar muhimmanci, gwamnati ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa tare da nuna wa al’ummar Kano cewa ba ɓigewa suke da ramukon gayya da cimma burukan su na siyasa maimakon yin adalci ba.
Sunana Haruna Abubakar Bebeji.
Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya. Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su.
Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci. Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.
A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina.
Na gode da ziyartar shafina.
Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.
Comments
Post a Comment