Shirin Yin Aiki (Tiyata) Kyauta ga Mata Masu Juna Biyu (CS) Yayin Haihuwa: Tsari Mai Matuƙar Mahimmanci ga Lafiyar Mata a Najeriya
#TasirinAliPate - Yabawa Farfesa Muhammad Ali Pate na Ƙaddamar da Sabon Shirin Yin Aiki (Tiyata) Kyauta ga Mata Masu Juna Biyu (CS) Yayin Haihuwa: Tsari Mai Matuƙar Mahimmanci ga Lafiyar Mata a Najeriya - Haruna Abubakar Bebeji
A wani gagarumin ci gaba na inganta kiwon lafiyar mata masu juna biyu a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa a yanzu za a fara yiwa mata masu juna biyu aikin tiyata (CS) kyauta a yayin haihuwa da buƙatar hakan ta taso ko matan da ke buƙata. Wannan sabon shiri da Babban Ministan lafiya da walwalar jama'a na Tarayyar Najeriya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya jagoranta, ya zo a matsayin wani babban hoɓɓasa da tabbatar da jajircewar gwamnati na rage yawan mace-macen mata masu juna biyu a wajen haihuwa a ƙasar nan.
Bayanin da Farfesa Pate ya yi kwanan nan ya jaddada hangen nesa dake ƙunshe a cikin manufofin kiwon lafiya, dake cikin Jadawalin Manufofin Sabuwar Fata wanda aka fi sani da "RENEWED HOPE" na Shugaba Bola Ahmad Tinubu. Wannan yunƙurin na nuna hangen da gwamnati tayi na irin ƙalubale ko taskun da mata masu juna biyu ke fuskanta, musamman waɗanda suka fito daga wurare masu rauni da kuma marasa galihu, waɗanda galibi ba sa iya ɗaukar matakan da suka dace. Kamar yadda Farfesa Pate ya bayyana a cikin jawabin sa mai cike da tausayawa, "Babu macen da za ta rasa ranta saboda rashin iya biyan kuɗin yi mata aikin tiyata yayin haihuwa (CS)" Wannan yunƙuri abun a yana ne da jin daɗi musamman ga al'ummar da a baya ba'a bada muhimmancin ga wannan ɓangare ba.
Shirin na rage mace-macen mata a yayin haihuwa wanda aka fi sani da Maternal Mortality Reduction Innovation Initiative (MAMII) shi ya samar da wannan ƙuduri mai matuƙar tasiri inda zai tabbatar da cewa matan da suke da buƙatar ayi musu aikin tiyata yayin haihuwa (CS) sun sami damar cin moriyar shirin a dukkanin asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu ko na ƴan kasuwa. Wannan yunƙurin ba wai kawai don ya kawo wani sabon tsari bane; yana tabbatar da burin samar da cigaba ne, mutuntawa da tausayawa mata masu juna biyu, da tallafa musu tare da ceto ransu, wanda ake rasa rayuka bila adadin a rashin irin wannan tsari a baya, a faɗin Najeriya. A cikin ƙasar da adadin mace-macen mata masu juna biyu ya kasance ya zarce misali, irin waɗannan matakan suna da mahimmanci don gina ingantacciyar al'uma.
Ba za a iya kwatanta irin muhimmancin da wannan sabon tsari zai kawo ba, musamman ma a cikin ƙasar da galibi samun ingantaccen lafiya ya ta'allaƙa ne da ƙarfin da mutum yake da shi na kuɗi. Bijiro da wannan shiri na yin tiyata ga masu juna kyauta ba wai kawai sabon ƙudurin kiwon lafiyar al'uma bane, har ma da samar adalci a zamantakewar al'uma. Hakan kuma shi yake tabbatar da damuwar da gwamnati ke da shi na halin da mata masu juna biyu ke ciki, tare da ba su kulawar da ya dace da kuma tabbatar da cewa rayuwarsu da na ƴaƴan da suke ɗauke da su a cikin su suna da matukar muhimmanci a wajen gwamnati.
Haƙiƙa salon jagorancin Farfesa Muhammad Ali Pate na manufofin kiwon lafiya ya bambanta da wasu manufofin kiwon lafiya da suka gabata. Yunƙurin da ya yi na magance matsalolin da ke haifar da mace-macen mata masu juna biyu, tare da nuna tausayinsa akan irin ƙalubalen da ƴan Najeriya ke fuskanta musamman mata, ya sa ya zamo na daban a matsayinsa na Minista da ya damu da al'uma da basu kulawa na gaskiya. Kyakkyawar ƙudurin sa na samar da daidaito wajen kiwon lafiyar al'uma, shine yazo daidai da irin ƙa'idojin da ake amfani da su a duniya a halin yanzu, musamman a ƙasashen da suka cigaba, wanda ke nuni da kyakkyawar hangen nesa da ya kamata ace tuntuni an samar a Najeriya.
Bijiro da wannan sabon tsari, haƙiƙa ya samar da wani sabon shafi na kula da lafiyar mata, inda babban burin da ake da shi, shine mai da hankali kan jin daɗin jama'a maimakon ɗora musu nauyin da mafiya yawan al'uma basa iya ɗauka. Ya kuma samar da wata kafa na kawo gyara a fannin kiwon lafiya, inda yayi kira ga gwamnatocin jihohi, cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ko na ƴan kasuwa, da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da wannan sabon shirin tare da kira a gare su, da su saka hannun jari a ɓangaren kiwon lafiyar mata.
A matsayinmu na ƴan kasa, ya zama wajibi mu yaba tare da nuns goyon bayan mu ga wannan sabon tsari mai matuƙar muhimmanci. Muna kira da a samar da zauren tattaunawa da zai wayar da kan jama'a game da wannan yunƙurin da haɓaka tsarin tallafawa al'umma wanda zai bada fifiko ga lafiya da tseratar da iyayen mu mata. Shirya taruka na wayar da kan al'uma zai ilimantar da mata game da ƙa'idojin cancanta da ƙarfafa musu gwiwa wajen kiwon lafiya ko neman kulawar da suke buƙata ba tare da fargabar matsalolin rashin kuɗi ba.
A ƙarshe muna jinjina wa Farfesa Muhammad Ali Pate bisa irin ƙoƙarinsa wanda shine irin sa na farko da aka yi na kare rayukan iyaye mata a Najeriya. Hasashensa ta hanyar shirin MAMII ya haifar da wani sabon nutsuwa ga ƴan ƙasa, ta fuskar kula da lafiyar mata masu juna biyu, tare da yin kira ga kowane ɗan Najeriya da ya gane cewa yayin da muke murnar wannan gagarumin shiri na cigaba, mu sani cewa, wannan somin taɓi ne na irin tsare-tsare na samar da ingantacciyar lafiya ga dukkan mata a Najeriya. Mu haɗa kai domin samar da kyakkyawar makoma ga iyayenmu mata, ƴan uwanmu, da ɗaukacin al'ummar mu baki ɗaya.
Sunana Haruna Abubakar Bebeji.
Nine Jami'in Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Masu Ruwa da Tsaki da Shigo da Al'umma na Ma'aikatar Lafiya da Jin Daɗin Al'umar Najeriya na Shiyyar Arewa maso Yamma.
Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya. Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su.
Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci. Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.
A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina.
Na gode da ziyartar shafina.
Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.
08034859051
08033064022
penbebeji.blogspot.com
ha.bebeji@gmail.com
Comments
Post a Comment