#TasirinAliPateAShekaraGuda

Tasirin Ali Pate: Shekara Ɗaya na Nasarori masu Mahimmanci da Kyakkyawan Jagoranci a Fannin Lafiya da Walwalar Jama'a a Najeriya - Haruna Abubakar Bebeji
A yayin da Najeriya ke cigaba da tafiya cikin sarƙaƙiyar yanayin kiwon lafiya, da jin daɗin jama'arta, yana da kyau a amince da muhimman nasarorin da aka samu a cikin ƙasa da shekara guda ƙarƙashin jagorancin Farfesa Muhammad Ali Pate. 
 
A cikin shekara ɗaya kacal, Farfesa Muhammad Ali Pate ya tabbatar da kansa a matsayin gwarzo na gaskiya a fannin kiwon lafiya da walwalar al'umar Najeriya.  A matsayinsa na Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate ya jagoranci tsare-tsare da dama da suka yi tasiri mai kyau a rayuwar miliyoyin ƴan Najeriya.
Farfesa Pate wanda Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya naɗa ya nunawa duniya cewa ba wai kawai shi ne mutumin da ya dace da wannan aiki ba, har ma ya kasance wani abin alfahari ga ɓangaren kiwon lafiya da jin daɗin al’umma.  Shekarar sa ta farko a kan wannan matsayi ta samu wasu sauye-sauye da ke nuna aniyarsa na inganta rayuwar ƴan Najeriya.

A ƙarƙashin jagorancinsa, Ma'aikatar Lafiya da Walwalar Al'uma ta Tarayya ta sami nasarori masu mahimmanci waɗanda suka kafa sabon ma'auni na ƙwarewa a fannin kiwon lafiya. Kama daga rattaba hannu kan manyan tsare-tsare da jihohi 36, da abokanan hulɗa, kamfanoni masu zaman kansu, da Ƙungiyoyin Sa kai (masu zaman kansu), har zuwa samar da Biliyoyin Daloli na alƙawurra daga abokan hulɗa, haƙiƙa Farfesa Ali Pate ya kasance zakaran gwajin dafi. 
Ingatattun Manufofi ga Fannin Kiwon Lafiya da Walwalar Jama'ar Najeriya  
Kasantuwar Farfesa Pate a matsayin Babban Ministan Lafiya da Walwalar Al'uma ya samar da kyawawan tsaruka da suke tattare da hangen nesa da samar da tabbaci. Tsarinsa ta samar da cikakkun hanyoyin fahimtar irin ƙalubalen da tsarin kiwon lafiya ke fuskanta a Najeriya tare da samar da sabbin hanyoyin warware matsalolin da ake da su don magance waɗannan ƙalubale yadda ya kamata. Tun daga rana ta farko da ya kama aiki, Farfesa Pate ya jaddada mahimmancin tsarin da ya dace a dinga bi, da kuma muhimmancin haɗin kai, don samun nasarar abinda aka sa a gaba, da tabbatar da cewa kafatanin ƴan Najeriya, ba tare da la'akari da matsayinsu na zamantakewa ko ƙarfin tattalin arziki ba, sun sami damar samun ingantaccen kiwon lafiya da walwalar su.

Muhimman Nasarorin da Ma'aikatar Lafiya da Jin Dadin Al'umar Najeriya ta samu

1. Ƙarfafa Kayayyakin Kiwon Lafiya: - Ɗaya daga cikin manyan nasarorin da Farfesa Pate ya samu shi ne gagarumin cigaban da aka samu a fannin kiwon lafiya a Najeriya.  A ƙarƙashin jagorancinsa, an gina sabbin asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da yawa, yayin da kayan aikin da ake da su sun sami cigaba mai yawa wajen samar da su da inganta waɗanda ake da su a ƙasa.  Wannan cigaban ba wai kawai ya faɗaɗa damar yin amfani da aikin kiwon lafiya ba ne, har ma ya tabbatar da cewa ana isar da waɗannan ayyukan cikin ingantacciyar hanya da kulawa da marasa lafiya yadda ya dace. 

2. Haɓaka Ƙwararrun Ma'aikata na Kiwon Lafiya: - Sanin cewa tsarin kiwon lafiya mai inganci yana dogara ne akan ma'aikatan da suka samu horo mai inganci, Farfesa Pate ya jagoranci shirye-shirye don ɗaukar ma'aikata, horar da waɗanda ake da su, da kuma riƙe ƙwararrun da muke da su a fannin kiwon lafiya. Ta hanyar haɗin gwiwa da manyan ƙungiyoyin kula da kiwon lafiya na duniya da cibiyoyin ilimi, Ma'aikatar ta sauƙaƙa shirye-shiryen horarwa na ƙara sanin makamar aiki ga likitoci, ma'aikatan jinya, da sauran ma'aikatan sashin kiwon lafiya. Wannan yunƙurin ya haifar da ƙara samun ƙwararrun ma'aikata waɗanda za su iya biyan buƙatun kiwon lafiyar al'umma.
Ɗaukar ma'aikatan lafiya sama da 2,400, da yiwa miliyoyin yara allurar rigakafin cututtuka daban-daban, da aiwatar da ayyukan samar da ababen more rayuwa sama da 200, da kuma sayan muhimman kayayyakin aikin jinya, kaɗan ne daga cikin irin gagarumin ayyukan da aka yi a ƙarƙashin kulawar Farfesa Ali Pate. 

3. Faɗaɗa Samar da Inshorar Lafiya: - A wani yunƙuri na samar da kiwon lafiya cikin sauƙi kuma a wadace, Farfesa Pate ya jajirce wajen faɗaɗa ayyukan hukumar inshorar lafiya ta ƙasa. Ya samar da sabbin tsare-tsare na inshorar lafiya da tabbatar da cewa ƴan Najeriya da dama, musamman waɗanda ke yankunan da aka barsu a baya ko aka musu nisa, da kuma yankunan karkara, za su iya samun muhimman ayyukan kiwon lafiya ba tare da fuskantar ƙunci na rashi ba. Wannan yunƙurin ya taimaka wajen rage kashe kuɗi, da dama ba a samu cikin sauƙi, da haɓaka ayyukan kiwon lafiya gaba ɗaya.
 
4. Magance Kalubalen Kiwon Lafiyar Al'uma: - Farfesa Pate ya kuma kasance kan gaba wajen magance matsalolin kiwon lafiyar jama'a da suka haɗa da cutar COVID-19, zazzaɓin cizon sauro, da matsalolin lafiyar mata da yara. Matakan sa kai-tsaye, irin su gangamin alluran rigakafi, ilimantar da jama'a da wayar musu da kai akan kiwon lafiya, da rarraba muhimman kayayyakin kiwon lafiya, sun daƙile yaɗuwar waɗannan cututtuka da kuma ƙara ƙarfin gwiwar al'ummar ƙasar wajen fuskantar barazanar kiwon lafiya.
 
Baya ga waɗannan nasarorin, Farfesa Ali Pate ya kuma ɗauki matakai na ƙarfafa tsarin doka, da amincewa da tsarin tafiyar da ma’aikatan lafiya da dawo da Ma'aikatan mu na lafiya da suka yi ƙaura gida Najeriya, da tabbatar da cewa asibitocin dake ƙarƙashin kulawar gwamnatin tarayya sun samar da kayan aikin da za su ba marasa lafiya ingantaccen kulawa da sauƙaƙa musu.
 
5. Sauye-sauye Da aka Samar na Jin Daɗi da Walwalar Al'uma: - Baya ga samar da kiwon lafiya, Farfesa Pate ya samu gagarumar nasarori wajen bunƙasa jin daɗi da walwalar ƴan Najeriya. Manufofinsa sun fi mayar da hankali kan inganta shirye-shiryen bada kariya na zaman take wa domin samun rayuwa mai inganci, tallafawa al'umma masu rauni, da inganta haɗin gwiwa wajen zamantakewa.  Shirye-shiryen da suka haɗa da bada tallafi na kuɗi, matakan samar da abinci, da bada tallafin karatu ga yara marasa galihu sun yi tasiri sosai wajen rage raɗaɗin talauci da inganta rayuwa ga yawancin ƴan Najeriya.

Samfurin Kyakkyawar Jagoranci 
Salon jagorancin Farfesa Pate ya kasance abin koyi, na gaskiya, riƙon amana, da haɗin gwiwa. Ya haɓaka al'adar gudanar da ayyuka a buɗe a cikin ma'aikatar, ƙarfafa haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki da shigo da al'umma a cikin hanyoyin yanke shawara don samun nasara. Wannan tsarin haɗaka ba wai kawai ya samar da gamsuwa ko gina amincewar jama'a bane kaɗai, har ma ya tabbatar da cewa manufofi da shirye-shirye sa, sun dace da buƙatun jama'a.

A bayyane yake cewa Tasirin Farfesa Ali Pate na gaskiya ne, kuma bayyananne, kuma Farfesa Pate shine irin mutumin da ya dace da aikin. Jajircewarsa, sha’awar sa, da sadaukarwarsa wajen inganta lafiya da jin dadin ƴan Nijeriya abin a yaba ne, domin sun cancanci yabo.
Abinda Aka Saka A Gaba 
A yayin da Farfesa Pate ke cika shekara ɗaya a matsayin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, a bayyane yake cewa ƙokarin da ya yi ya kafa wani ginshiƙi na cigaba. Nasarorin da ya samu a cikin shekara guda kacal na nuni da irin ƙwazon da yake da shi na inganta lafiya da jin daɗin ɗaukacin ƴan Najeriya. A yayin da yake cigaba da wannan aiki mai muhimmanci, yana da kuma muhimmanci a cigaba da ɗora wannan cigaba da aka samu, da kuma ginawa akan waɗannan Nasarorin, don tabbatar da ɗorewar sa na dogon zango a fannin kiwon lafiya da jin daɗin jama'a.

A yayin da muke murnar cika shekara guda da Jagorancin Farfesa Ali Pate a Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Al'umar Najeriya, yana da kyau mu gamsu da irin gagarumin nasarorin da aka samu tare da fatan samun ƙarin nasarori masu yawa a shekaru masu zuwa. Lallai Najeriya ta yi sa'a da ta samu Mutum mai kishinta akan wannan muƙami, kuma muna fatan abin da ya soma zai cigaba da haifar da kyakkyawan canji da wanzar da sauyi mai ɗorewa a fannin kiwon lafiya. 

A ƙarshe, Farfesa Muhammad Ali Pate ya tabbatar da cewa shi ne mutumin da ya dace da aikin. Jagorancinsa, hangen nesa, tare da sadaukar da kai ga kiwon lafiya da zamantakewar ƴan Najeriya, tuni ya fara tasiri. A yayin da muke bikin shekararsa ta farko a ofis, muna ɗokin shaida wasu nasarorin mafiya girma a shekaru masu zuwa. #TheAliPateEffect ba kawai take ba ne;  wannan shaida ce ta sauyi da aka samu na ingantaccen jagoranci da kuma kyakkyawar makoma ga Nijeriya.

Sunana Haruna Abubakar Bebeji.

Nine Jami'in Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Masu Ruwa da Tsaki da Shigo da Al'umma na Ma'aikatar Lafiya da Jin Daɗin Al'umar Najeriya na Shiyyar Arewa maso Yamma. 

Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya.  Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su. 

Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci.  Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.  

A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina. 

Na gode da ziyartar shafina.

Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.

penbebeji.blogspot.com 
ha.bebeji@gmail.com 

Comments

Popular posts from this blog

CELEBRATING KANO STATE'S MONUMENTAL ACHIEVEMENTS UNDER GOVERNOR AKY

MUHAMMADU SANUSI II'S BETRAYAL OF PEOPLE'S TRUST

JUSTICE SERVED: TRUTH PREVAILS AS RAHAMA SAIDU'S TIKTOK CLAIMS DEBUNKED