#TasirinAliPateAShekaraGuda
Tasirin Ali Pate: Shekara Ɗaya na Nasarori masu Mahimmanci da Kyakkyawan Jagoranci a Fannin Lafiya da Walwalar Jama'a a Najeriya - Haruna Abubakar Bebeji A yayin da Najeriya ke cigaba da tafiya cikin sarƙaƙiyar yanayin kiwon lafiya, da jin daɗin jama'arta, yana da kyau a amince da muhimman nasarorin da aka samu a cikin ƙasa da shekara guda ƙarƙashin jagorancin Farfesa Muhammad Ali Pate. A cikin shekara ɗaya kacal, Farfesa Muhammad Ali Pate ya tabbatar da kansa a matsayin gwarzo na gaskiya a fannin kiwon lafiya da walwalar al'umar Najeriya. A matsayinsa na Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate ya jagoranci tsare-tsare da dama da suka yi tasiri mai kyau a rayuwar miliyoyin ƴan Najeriya. Farfesa Pate wanda Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya naɗa ya nunawa duniya cewa ba wai kawai shi ne mutumin da ya dace da wannan aiki ba, har ma ya kasance wani abin alfahari ga ɓangaren kiwon lafiya da jin daɗin al’umma. Shekarar sa ...