WAIWAYE AKAN KWANAKI 30 NA MULKIN SHUGABA TINUBU

Irin Matakan da Shugaba Tinubu yake Ɗauka na Bada Kyakkyawar fata ga makomar Najeriya –Haruna Abubakar Bebeji
Gabatarwa:

A kwanaki 30 da suka gabata, Najeriya ta samu sauyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin shugaba Tinubu. An samu tsauraran ƙudurori da ɗaukar matakai masu tsauri, wanda zai share fagen kawo sauyi mai amfani ga al'umma. Duk da yake waɗannan sauye-sauyen sun haifar da wahalhalu da tsadar rayuwa, amma yana da muhimmanci a gane manyan ayyuka masu tasiri da shugaba Tinubu ya yi da kuma yuwuwar da suke da shi na maido da martabar Najeriya.

Bijiro da Tagwayen Ƙudurori wajen Ƙoƙarin Ƴanta Najeriya daga Ƙangin Talauci

Manufofin shugaba Tinubu na ƴantar da al'umar Ƙasar nan, da suka haɗa da cire tallafin man fetur da kuma yin garambawul ga kuɗin Najeriya ta hanyar daidaita farashin kuɗin ƙasashen waje da ake yi da canjin kuɗi na Naira, lamarin da ya girgiza sassa daban-daban na tattalin arzikin ƙasar.  Abubuwan da suka biyo bayan waɗannan manufofin sun kawo ƙalubale ga gidaje, kasuwanci, da tattalin arziƙin baki ɗaya. Duk da haka, yana da muhimmanci a fahimci hikima da hangen nesa da Shugaba Tinubu ke da shi na ɗaukar waɗannan tsauraran matakai da manufofin dake tattare da shawarwarin da ya yanke.
Sake fasalin Tattalin Arzikin Nijeriya:

1. Faɗuwar darajar Naira da hauhawar farashin kayayyaki: Babu shakka cigaba da faɗuwar darajar Naira da hauhawar farashin kayayyaki ya sanya mutane da yawa cikin wahala. Amma duk da haka, waɗannan sauye-sauye na daidaita farashin kuɗin ƙasashen waje da gwamnatinsa ta yi wanda ya karya darajar Naira, da kuma kawar da tallafin da gwamnati ke fitarwa na man fetur zai haifar da ingantaccen tattalin arziki mai ƙarfi.  Yayin da za a bar  kasuwanni na bayan fage suci gaba da tsayar da farashi da cin gashin kansu, Naira za ta samu darajar da ta dace, wanda zai ƙarfafa gwiwar masu zuba jari da kuma bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa.
 2. Matsalar Makamashi da Samar da Wutar Lantarki: Ba ɓoyayyen abu ba ne cewa Najeriya na fuskantar ƙalubale a bangaren makamashi.  Ci bayan da aka samu na samar da wutar lantarki ya dagula al'amura. Duk da haka, wannan matsalar ya ba da damar yin gyare-gyare mai ƙarfi a fannin makamashi.  Gwamnatin Shugaba Tinubu ta himmatu wajen nemo hanyoyin da za a bi na dogon lokaci, da tabbatar da ingantacciyar hanyar samar da makamashi da samar da yanayin da zai dace da saka hannun jari.

Kyawawan Alamomi masu Ƙarfafa Gwiwan Ƴan Ƙasa:

Duk da koma bayan da aka samu a baya, a yanzu akwai alamu masu kyau game da makomar Najeriya a ƙarƙashin jagorancin shugaba Tinubu.  Abubuwa da yawa suna nuna alamun kyakkyawar makoma ga ƙasar:
 1. An samu Inganci a Kasuwannin Hannayen Jari: Kasuwannin hannayen jari sun samu gagaruman nasarori da suka haura kashi 13.5%, inda masu zuba jari suka samu ribar Naira tiriliyan 3.9. Wannan ƙaruwar tana nuna ƙwarin gwiwa game da ƙarfin tattalin arzikin Najeriya kuma yana aika saƙo mai kyau ga masu zuba jari na cikin gida da na waje.

 2. Juyo da Hankalin Masu saka hannun jari: Matakan da Gwamnati take ɗauka na ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar nan sun ja hankalin masu saka hannun jari wanda a baya suka bar ƙasar.  Komowar suna nuni da gamsuwar su kan farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya da yuwuwar samar da kyakkyawan sakamako.
 3. Samun Rance da Gyaran Fannin Mai: Bankin Amurka ta bayyana yiyuwar inganta bada rance ga Najeriya, wanda ke nuna ƙwarin gwiwar masu zuba jari kan manufofin sabuwar gwamnati.  Hukumomin ƙasa da ƙasa sun kuma yi hasashen sake fasalin fannin man fetur da ake buƙata a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, wanda zai samar da damammaki masu yawa da kuma samar da ci gaba.

Ƙarshe:
 
Yayin da kwanaki 30 na farko na gwamnatin shugaba Tinubu ya sanya ƴan Najeriya da dama cikin matsin rayuwa, yana da matuƙar muhimmanci a gane manufofi da hikimar dake tattare da irin tsauraran matakan da yake ɗauka. Waɗannan matakai da yake ɗauka za su ba da damar sake farfaɗo da martabar Najeriya a tsakanin takwarorinta a duniya. Yayin da al'ummar ƙasar ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen da shirin ƴantar da tattalin arzikin Najeriyan ke kawowa, yana da matuƙar muhimmanci a cigaba da kyautata zaton nan gaba zata kai matakin da muke fata. Yunƙurin da shugaba Tinubu yake yi na maido da martabar Najeriya da kuma mayar da ita kan turba, na ƙara ƙarfafa da sabunta fatan cewa sadaukarwar da ake yi a yau za ta samarwa da al’umma ɗumbin albarkatu da wadata a gobe.
Sunana Haruna Abubakar Bebeji.

Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya. Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su. 

Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci. Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.  

A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina. 

Na gode da ziyartar shafina.

Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.

Comments

Popular posts from this blog

JUSTICE SERVED: TRUTH PREVAILS AS RAHAMA SAIDU'S TIKTOK CLAIMS DEBUNKED

SANUSI BATURE, AN ACCIDENTAL SPOKESMAN: THE REJOINDRER

#TheAliPateEffect - A Milestone for Maternal Health in Nigeria