TSOFAFFIN GWAMNONI BASU CANCANCI SHIGA CIKIN JERIN MINISTOCI BA
Naɗin Ministoci: Dole ne Shugaba Tinubu ya ba da fifiko a kan Cancanta bisa Alaƙar jam’iyya a Naɗin Muƙamai – Haruna Abubakar Bebeji
Gabatarwa:
Yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da jiran naɗin ministocin da shugaba Tinubu zai fitar, yana da matuƙar muhimmanci ya fifita cancanta da riƙon amana a kan wasu abubuwa. Tsofaffin gwamnoni da ƴan koren su, waɗanda suka yi wa kansu tabo da tambarin almundahana da cin hanci da rashawa, bai kamata a ce sun shiga cikin jerin sabbin ministoci da za'a naɗa ba. Domin cika alƙawarinsa na tabbatar da nagartattun mutane masu basira da gogewa sun ba da gudummawar cigaban Najeriya, dole ne Shugaba Tinubu ya yi watsi da matsin lamba daga wasu ƴan koren jam’iyya, maimakon haka ya mai da hankali kan shigo da sabbin mutane masu basira waɗanda ba su da wani tabo na cin hanci da rashawa.
Cire tsofaffin gwamnoni daga cikin jerin waɗanda zasu ƙunshi majalisar zartarwar sa, zai kasance kyakkyawar shawara mataki, idan aka yi la’akari da zargin cin hanci da rashawa da ya dabaibaye su. Yanke wannan shawarar zai tabbatar da kyakkyawar makoma ga Nijeriya, ba tare da anyi kitso da ƙwarƙwata da waɗanda suka yi shuhura wajen almundahana da dukiyar al'uma ba.
Sauka daga Tsohuwar Turba zuwa Rungumar Sabon Layi:
Ba ɓoyayyen abu bane cewa da yawa daga cikin tsofaffin gwamnonin sun gaza cika alƙawuran da suka ɗauka a jihohin su da cimma burin da aka sanya musu, maimakon haka sun fifita buƙatun su kan cigaban jihohinsu. Yanzu ne lokacin da Shugaba Tinubu zai sake ɓullo da wani sabon salo ta hanyar ƙin sanya su a ƙunshin Majalisar Zartarwar sa. Muna buƙatar sabbin fuskoki, marasa gurɓatattun tarihin badaƙalar cin hanci da rashawa, waɗanda suke da cancanta da ƙwarewa na tafiyar da manufofin cigaban ƙasa.
Ƙwarewa da Gogewa:
Shugaba Tinubu ya samu kyakkyawar shaidar zaƙulo masu hazaƙa da haɗa gungun mutane masu inganci tattare da shi. Ya zama wajibi ya cigaba da wannan ɗabi’a yayin kafa majalisar ministocinsa, tare da tabbatar da cewa an zaɓo waɗanda suke da cancanta ne kawai. Ta yin haka, zai nuna ƙwazonsa na ganin an ciyar da Najeriya gaba da kuma daƙile tunanin cewa alaƙar siyasa ta fi tasiri akan cancanta wajen rabon muƙamai.
Ta hanyar kaucewa al’adar shigar da tsofaffin gwamnoni cikin majalisar zartaswa, Shugaba Tinubu zai iya shigo da mutane masu hazaƙa. Samar da Ministoci zaɓe bisa la'akari da cancanta da tantance waɗanda suke da gogewa a fannoni daban-daban zai tabbatar da samar da ƙwararrun mutane da zasu iya haifar da canji mai ma'ana a Najeriya.
Bada Dama Ga Sabbin Fuskoki:
Cin hanci da rashawa ya kasance babban ƙalubalen da aka daɗe ana fama da shi a Najeriya. A yayin da ƙasar ke ƙoƙarin shawo kan wannan ƙalubalen, yana da matukar muhimmanci a tabbatar da gaskiya da riƙon amana a dukkan ɓangarorin gwamnati. Amma duk da haka, a mafiya yawan lokuta, an fi samun tsofaffin da hannu dumu-dumu wajen cin hanci da rashawa, sun zubar da mutuncinsu tare da kawo tasgaro ga cigaban al’umma.
Tun daga sama da faɗi da karkatar da kuɗaɗen jihohin su domin amfanin kansu da rashin adalci, tsofaffin gwamnonin sun shafawa kansu ɓaƙin fenti da zubar da kimar su a wajen al'umomin da suka jagoranta. Bisa la’akari da haka, ya zama wajibi shugaba Tinubu ya fito da wani sabon tsari da kuma nuna aniyar tabbatar da tsaftataccen shugabanci ta hanyar ƙin sanya su cikin majalisarsa.
Ta hanyar ƙin sanya tsofaffin gwamnoni a cikin majalisar ministocinsa, Shugaba Tinubu zai aika da wani saƙo mai ƙarfi cewa zamanin cigaba da amfani da Shugabannin da ke da zarge-zarge a kansu ya wuce. Wannan mataki zai sa jama'a su amince cewa da gaske yana son abin da zai dace ya kuma taimaki ƙasar. Haka kuma, hakan zai ba da damar samun sauyi, wanda zai baiwa sabbin mutane masu sabbin dabaru da ƙwarewa wajen baje kolin ƙwarewarsu da bayar da gudummawa mai ma'ana ga cigaban Najeriya.
Tsoffin Gwamnoni basu cike ƙa'idojin Cancanta Ƙwarewar da ake Buƙata ba:
Saɓanin yadda ake tunanin cewa tsofaffin gwamnoni ne kawai ke da cancantar shugabanci, Allah Ya albarkaci Najeriya gogaggun mutane a kowace jiha waɗanda zasu iya sauke nauyin da za'a ɗora musu. Waɗannan haziƙan mutane, waɗanda ba su da wani tabo na cin hanci da rashawa, sun cancanci a ba su dama domin ba da tasu gudummawar ga cigaban al’umma.
Ra'ayi mafi rinjaye na ƴan Najeriyar dai shi ne cewa waɗannan tsaffin gwamnonin ba zasu fifita muradun cigaban ƙasa ba, kuma galibi abubuwan da suke yi don amfanar kansu da Iyalan su ne kawai. Don haka ya zama wajibi shugaba Tinubu ya saurari koke-koken jama’a ya kuma kula da damuwarsu.
Domin ciyar da Najeriya gaba, yana da muhimmanci a samar da yanayi mai kyau ga cigaban Najeriya. Shigo da tsofaffin gwamnoni a majalisar zartarwar zai sa aci gaba da tsarin yin almundahana ne ga al'uma, da wanzar da cin hanci da rashawa wanda zai dabaibaye gwamnatin, wanda hakan zai kawo cikas ga cigaban al’umma.
Ƙarshe:
Dole ne shugaba Tinubu ya yi watsi da yunƙurin tsoffin gwamnoni da ƴan korensu da ke neman muƙaman ministoci. Ta hanyar ba da fifiko kan cancanta fiye da la'akari da alaƙar jam’iyya da kuma hana mutanen da ke da zarge-zargen cin hanci da rashawa dama, hakan zai nuna jajircewarsa ga sabon fatan da al'uma ke da shi a wannan gwamnati.
Wannan mataki dai ba wai kawai zai kafa tarihi ne da nuna hanya ga shugabanni masu zuwa ba, har ma zai ƙara ƙarfafawa jama'a gwiwa da masu ra'ayin cewa cigaban Najeriya ba zai samu ba sai ta hanyar naɗa mutane masu ƙwarewa da kuma son yi wa ƙasa hidima. A yayin da shugaba Tinubu yake gudanar da wannan muhimmin aiki, dole ne ya tuna cewa makomar Najeriya ta dogara ne kan yadda ya iya sanya mutanen da suka dace a kan muƙamai da zasu tafiyar da gwamnatin sa.
Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya. Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su.
Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci. Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.
A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina.
Na gode da ziyartar shafina.
Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.
penbebeji.blogspot.com
ha.bebeji@gmail.com
Comments
Post a Comment