SANATA BABANGIDA HUSSAINI KAZAURE: YANKIN JIGAWA TA AREWA MASO YAMMA TA DACE DA JAJIRTACCEN WAKILI

Sanata Babangida Hussaini Kazaure: Jajirtaccen Wakilin Shiyyar Jigawa ta Arewa Maso Yamma - Haruna Abubakar Bebeji
Gabatarwa:

A fagen siyasar Najeriya, sau da yawa abu ne mai wuya a samu wakilin da ya samu kyakkyawar shaidar yiwa al'uma hidima, sadaukarwa, da kishin kasa tun kafin ya samu damar wakilci. Sai dai Sanata Babangida Hussaini Kazaure, wanda aka fi sani da Walin Kazaure, ya tsaya tsayin daka a matsayinsa na fitaccen mutum wanda a koda yaushe yake nuna jajircewar sa wajen kyautata rayuwar al’ummar yankin sa. Ƙwararre a sha'anin tafiyar da harkokin gwamnati da kuma kyakkyawan tarihi da ya kafa a matsayinsa na tsohon Babban Sakatare (Permanent Secretary) a ma’aikatun gwamnatin Jiha da ta Tarayya, Sanata Kazaure a Zaɓen da aka yi kwanan nan, ya samu nasara a matsayin Sanata mai wakiltar Shiyyar Jigawa ta Arewa maso Yamma wanda hakan ke nuna cewa Shiyyar zata ci moriyar kyakkyawan wakilci nagari da zai bunƙasa yankin.

Rayuwar Aikin Gwamnati mai Cike da Nasara:
Shuhura da fice da Sanata Babangida Hussaini Kazaure yayi yana aikin gwamnati, ya kai na tsawon sama da shekaru talatin, tun daga sanda ya fara aiki a tsohon gwamnatin jihar Kano. Yayi ta samun cigaba a matsayi da muƙamai, inda bayan an ƙirƙiri Jihar Jigawa daga tsohuwar Jigawa, ya koma Jihar tasa ta asali inda ya fara aiki a ofishin ma’aikata na musamman na Jihar Jigawa (Cabinet Office), inda bajinta, ƙwazon sa da sanin makamar aiki yasa yayi ta samun ƙarfin girma har zuwa maƙura na matakin Babban Sakatare (Permanent Secretary) a 2002. Bisa la’akari da ƙwarewarsa a harkokin gudanarwa, tsare-tsare na ilimi, da ci gaban al’umma, ya samu shaida da lambobin yabo da dama, ciki har da karrama shi a matsayin wakilin Ƙungiyar Masu Kiyaye Haɗuran dake Addabar Lafiya na Nijeriya wato Fellow of the Occupational Safety and Health Association, Nigeria. 
Burinsa na Ciyar da Al'uma Gaba :
A lokacin yaƙin neman zaɓensa, Sanata Kazaure ya zayyana muhimman abubuwa guda uku da zai fi mayar da hankali a kansu idan ya samu nasara, sune: kiwon lafiya, samar da tsaftataccen al’umma da samar da ilimi. Ya damu ƙwarai da ƙalubalen da al’ummar mazaɓarsa ke fuskanta, inda yayi alƙawarin bada kulawa da tabbatar da yayi abinda ya dace a waɗannan bangarori domin samar da ingantacciyar rayuwa ga kowa da kowa. A matsayinsa na tsohon Babban Sakatare ko Sakatare na dindindin, Sanata Kazaure yana da hazaƙa da gogewa, wanda hakan ya ba shi damar tafiyar da sarkakiyar tafiyar da mulki da kuma samar da kyakkyawar sakamako.

Amanar da ya ƙulla da al'uma:
Ɗaya daga cikin kyawawan halayen Sanata Babangida Hussaini Kazaure shine jajircewarsa na yiwa al'umma hidima. Duk da irin gudunmawa ya bayar da cigaban da ya samar a mahaifar sa ta Kazaure,, sadaukarwar sa ta wuce iyakokinta, har ya kai ga sauran masarautun jihar Jigawa da ma sauran wurare. Ayyukan sa na jin ƙai da ya keyi ya ƙara ɗaukaka sunansa a matsayinsa na fitaccen ɗan kishin ƙasa, wanda ya himmatu wajen tunkarar manyan matsalolin da ke tunkarar al’ummar mazaɓarsa a karni na 21.
Buɗaɗɗiyar Wakilci:
A yayin yaƙin neman zaɓen sa, Sanata Kazaure ya jaddada muhimmancin haɗa kai da gudanar da buɗaɗɗiyar wakilci. Ganin irin rawar da ingantaccen wakilci ke takawa wajen magance buƙatu da muradun jama’a, ya yi alƙawarin yin cudanya da jama’ar mazabarsa, da sauraron damuwarsu, da kuma bayyana ra’ayoyinsu a zauren majalisar dattijai na ƙasa. Haƙiƙanin manufofin sa na haɗa kai da jin koken al'uma shi ke tabbatar da cewa zai bada fifiko da wajen ganin ya kyautatawa al'uma da cika burin da suke da shi a tsawon wa'adinsa na wakilci.

Buƙatar a Marawa Sanata Kazaure Baya:
Da kyakkyawan tarihi da ya kafa, da kuma jajircewar sa wajen kyautata rayuwar al'ummar mazaɓar sa, Sanata Babangida Hussaini Kazaure ya zamo wani Wakili da al'umar sa ke ganin zai haskaka rayuwar al'umar mazabar Jigawa ta arewa maso yamma. A yayin da yake shirin aiwatar da ayyukan raya ƙasa masu amfani daidai da burin al’ummarsa, ya zama wajibi mazauna yankin Jigawa ta Arewa maso Yamma da su marawa sabon wakilin nasu baya. Ta hanyar goyon bayan Sanata Kazaure, suna da ƙwararren mai fafutukar kare muradun su da kuma ba da gudummawa sosai ga ci gaban su da ci gaban yankin.
Ƙarshe:

Haƙiƙa Zaɓen Sanata Babangida Hussaini Kazaure a matsayin Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma abin a yaba ne, da kuma kyakkyawan fata ga al'umar yankin. Duba da irin nasarorin da ya samu da kyakkyawar tarihi da ya kafa a ɓangaren aiki da hidimtawa al'uma, Wakilin ya shirya tsaf don samar da ayyuka da zasu yi tasiri mai ɗorewa a babban zauren majalisar dokokin ƙasar. Akwai buƙatar al'umar mazaɓan sa, a matsayinsa na Wakilin su, su marawa Sanata Kazaure baya, domin yin hakan, shi zai bawa Wakilin nasu ƙwarin gwiwar yin aiki tukuru don ganin an kawo sauyi mai kyau da kyakkyawar makoma ga kowa.
Sunana Haruna Abubakar Bebeji.

Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya.  Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su. 

Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci.  Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.  

A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina. 

Na gode da ziyartar shafina.

Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.
ha.bebeji@gmail.com 

Comments

Popular posts from this blog

JUSTICE SERVED: TRUTH PREVAILS AS RAHAMA SAIDU'S TIKTOK CLAIMS DEBUNKED

SANUSI BATURE, AN ACCIDENTAL SPOKESMAN: THE REJOINDRER

#TheAliPateEffect - A Milestone for Maternal Health in Nigeria