MATAIMAKIN SHUGABAN ƘASA SHETTIMA YA ZIYARCI JIHAR SOKOTO: YA NEMI SHUGABANNIN AREWA SU HAƊA KAI

MATAIMAKIN SHUGABAN ƘASA SHETTIMA YA ROKI SHUGABANNIN AREWA SU HAƊA KANSU TARE DA GOYON BAYAN GWAMNATIN TINUBU DON MAGANCE MATSALAR TSARO, DA SAURAN ƘALUBALE.
Sultan yayi alƙawarin bada goyon bayan shirye-shirye da manufofin Gwamnatin Tarayya

Mataimakin shugaban ƙasa, Sen. Kashim Shettima ya yi kira ga shugabannin yankin arewa maso yammacin ƙasar nan da su haɗa kai su marawa ƙoƙarin gwamnati mai ci na magance ƙalubalen da ke fuskantar al’umma.

Mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan kiran ne a ranar Jumu'a a jawabin sa a lokacin da ya kai ziyarar gaisuwar Sallah ga mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar II a fadar sa.

A cewar sa, “Shugaba Tinubu yana sane da ƙalubalen da mutanen mu ke fuskanta – matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin Arewa maso Yamma, kuma yana ɗaukar matakai masu muhimmanci don magance lamarin.

"Ina kira ga shugabannin siyasar mu da su haɗa kai domin tunkarar ƙalubalen da muke fama da su, waɗanda suka haɗa da rashin tsaro, talauci da rashin ci gaba a yankin."
Yayin da yake miƙa saƙon taya murnar barka da Sallah na shugaba Tinubu, mataimakin shugaban ƙasan ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai, inda ya bayyana cewa "ba za a taɓa samun zaman lafiya ba, in babu cigaba, kuma ba za a taɓa samun cigaba ba in babu zaman lafiya."

Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu bisa amincewa da irin rawar da sarakunan gargajiya ke takawa, ta jajirce wajen basu duk taimakon da ya dace don bayar da tasu gudunmawar cigaban ƙasa.

Mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya kuma ja hankalin gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Ahmed Aliyu Sokoto don ganin ya jajirce wajen samar da shugabanci mai ma’ana tare da yi masa gargaɗi da yaci gaba da kyautata alaƙa tsakanin sa da shugabanni a faɗin jihar.

Da yake jawabi tun farko a wajen wata ƴar gajeriyar liyafar da aka yi wa mataimakin shugaban ƙasan a gidan gwamnati, Gwamna Aliyu Sokoto ya nuna jin daɗin sa da ziyarar, inda ya bayyana wannan karimcin da mataimakin shugaban ƙasar ya yi a matsayin nuna soyayya ga jihar Sakkwato da al’ummarta.

Ya bayyana mataimakin shugaban ƙasa Shettima a matsayin mutum mai haƙuri, juriya da jajircewa, yana mai tabbatar masa da goyon bayan jihar domin samun nasarar gwamnatin Tinubu.
A nasa ɓangaren, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya miƙa godiyarsa ga Mataimakin Shugaban ƙasan bisa wannan ziayar gaisuwar Sallah da ya kawo, inda yayi addu’ar Allah ya ba shi basira da ƙarfin ikon sauke nauyin da aka ɗora masa a matsayinsa na lamba biyu a ƙasar nan.

Sarkin Musulmin ya yabawa Gwamnatin Tarayya bisa irin matakan da take ɗauka Sannu halin yanzu na magance ƙalubalen da ke addabar al’ummar ƙasar nan, inda ya ce “daidai ne ɗaukar matakai tun yanzu, duk da matsin da za'a fuskanta, yana mai jaddada cewa tasiri da nasarorin da matakan zasu haifar nan gaba yafi muhimmanci.

Sarkin Musulmin ya yi alƙawarin cewa Masarautar sa zata marawa manufofi da shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya, inda ya ba da tabbacin cewa “muna goyon bayan ku 100% a kowane lokaci kuma muna tabbatar muku da hakan, za mu yi duk abin da ya kamata don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin ƙasar mu Najeriya."

Sauran manyan baƙi da suka halarci ziyarar gaisuwar Sallan sun haɗa da, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno;  Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Idris Gobir; Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa Sen. Aliyu Wamakko; Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Sen. Ibrahim Hassan Hadejia; Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa (Shiyyar Arewa), Sen. Abubakar Kyari da kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto, Rt.  Hon. Tukur Bodinga da dai sauransu.

 

Comments

Popular posts from this blog

JUSTICE SERVED: TRUTH PREVAILS AS RAHAMA SAIDU'S TIKTOK CLAIMS DEBUNKED

SANUSI BATURE, AN ACCIDENTAL SPOKESMAN: THE REJOINDRER

#TheAliPateEffect - A Milestone for Maternal Health in Nigeria