RUSHE SHATALETALEN GIDAN GWAMNATIN KANO DA ABBA K. YUSUF YAYI: CIN MUTUNCI GA AL'UMMAR JIHAR KANO
RUSHE SHATALETALEN GIDAN GWAMNATIN KANO DA ABBA K. YUSUF YAYI: CIN MUTUNCI GA AL'UMMAR JIHAR KANO - Haruna Abubakar Bebeji
Abin takaici ne yadda Abba Rusau ya ɗauki wannan matakin na ruguza wannan katafaren ginin na shataletalen gidan gwamnati, wanda gini mai fito da tarihin jihar Kano da al'umar ta da kuma bunƙasa al'adar mu musamman ta ɓangaren taswirar ɗabbaƙa al'adar mu, amma a dare ɗaya ala lalata shi saboda tsabar gilli da wani salo na rashin kishin al'uma da dukiyar su.
Wannan shawara da ya yanke na rashin tunani tsantsar cutarwa ce ba wai ga fasihiyar yarinyar da ta yi aiki tukuru wajen samar da irin wannan fasaha na birgewa ba, har ma ga al’ummar Jihar Kano da suka yaba da wannan gagarumin aikin na fasaha a wurinta. Ba wai kawai sun yi hasarar rushe shataletalen ba ne, har ma da tunani da dalilin da yake tattare da taswirar na jaddada kyakkyawar tarihin Kano.
Wannan ɗanyan aikin ko aika-aika ba wai almubazzaranci da dukiyar al’umma ba ne kaɗai, har ma da cin mutunci ga al’ummar Jihar Kano. Wannan shataletalen alama ce ta ci gaban da Jihar Kano ta samu da ɗabbaƙa al'adun mu, kuma an yi shi ne don zaburar da al'ummar mu wajen dagewa domin ƙirƙirar sabbin fasahohi. Hakan ya kasance shaida ce akan irin bajintar da al'umar mu ke da shi na ƙirƙire-ƙirƙire da hazaƙa na matasa masu zane-zane a Najeriya, kuma rushewar tana aika da saƙon cewa gudunmawar da suke bayarwa ba ta da amfani.
Matakin na Gwamna Abba Yusuf ya kuma kafa tarihi maras kyau, domin yana nuni da cewa ayyuka da tsare-tsaren cigaba da wata gwamnatin ta kawowa al'uma za a iya watsi da su kawai saboda gwamnatin da ta gabata ce ta fara aiwatar da su. Wannan ba wai kawai gajeriyar tunani ba ne ko rashin hangen nesa, hakan zai kawo cikas ga gwamnatoci masu zuwa wajen yunƙurin kawo ayyukan cigaba da zai amfanar da al'uma.
Bugu da ƙari, rusa ginin shataletalen na gidan gwamnati da aka yi kamar yadda na zayyana a baya, almubazzaranci ne da dukiyar al'umma. Kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen tafka wannan ɗanyan aikin mara amfani, za a iya karkatar da su domin ƙara samar da wasu ayyuka na cigaba da al'umar Jihar Kano suke da buƙata, kamar ilimi, kiwon lafiya, da haɓaka ababen more rayuwa. Matakin rusa wannan katafaren ginin mai cike da tarihi gazawar shugabanci ne da kuma cin Amanar da al'ummar jihar Kano suka baiwa Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Har ila yau, ya kamata a lura da cewa an rushe wannan katafaren shataletalen mai cike da tarihi ne ba tare da tuntuɓar al’ummar jihar Kano ba. Shawara ce da Maigirma Gwamnan ya yanke a karan kansa ko domin biyan buƙatar kansa ko na uban gidansa na siyasa da a wani irin yanayi yake mulkin jihar Kano a karo na uku wato, Rabi’u Musa Kwankwaso, ba tare da la’akari da ra’ayi da tunanin al'ummar Jihar Kano ba ko tunanin abinda rushewar za ta shafa kai tsaye ba.
Duk da yake kowa ya san gwamnonin suna da hurumin yanke shawara kan yadda za su tafiyar da jiharsu, amma matakin na Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shafi al'uma musamman idan mutum ya yi la’akari da dalilinsa na yanke wannan matsaya. Ko da yake ya yi iƙirarin cewa rusau da yake yi yana yinsu ne domin kawo sabbin sauye-sauye, amma GASKIYAR magana ita ce, yana wannan rushe-rushe ne kawai domin kawai ayyuka ne wanda ya gabace shi, Gwamna Ganduje ya kafa, kuma ya gina shi.
A ƙarshe dai matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na ruguza wannan shataletale da ya fito da tarihin Kano da al'umarta taɓargaza ne, kuma aiki ne na rashin tunani ko gajerar tunani da ba ta da wata manufa face cimma muradun kansa ko na uban gidan sa. Almubazzaranci ne da dukiyar al’umma, cin mutunci ne ga al’ummar Jihar Kano, da cin amanar da ‘yan jihar suka damƙa masa. Ina fata Gwamna Yusuf a nan gaba idan zai yi irin wannan taɓargaza ya dinga tunani da tuntuɓa, ya kuma ɗora ɗamarar kawo ayyukan ci gaba ga jihar Kano, maimakon ƙoƙarin janyowa kansa baƙin jini domin farantawa wani.
Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya. Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su.
Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci. Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.
A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina.
Na gode da ziyartar shafina.
Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.
Comments
Post a Comment