MALAM MAI ƁAROTA
Garo Ya Tafi, Garo Ya Dawo... Wa zai binciki wani? Kanawa Ana wasa da ƙwaƙwalen ku! - Malam Mai Ɓarota
A bisa dukkan alamu, a Jihar Kano babu waɗanda suka fi Cancanta su Jagoranci Ma'aikatar Ƙananan Hukumomi sai ƴan Ƙaramar Hukumar Kabo, a Kabon ma ƴan garin Garo, a Garon ma ƴan gida ɗaya, wanda hakan ke tabbatar mana da cewa suna da gogewa na sha'anin sanin makamar aikin Ma'aikatar Ƙananan Hukumomi.
Idan zamu iya tunawa, ɗan Takarar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano a Jam'iyyar APC, Murtala Sule Garo shi ya riƙe Ma'aikatar na shekaru takwas a gwamnatin da ta gabata kafin ya sauka don takara. A wannan karon ma da babban Jam'iyyar adawa ta NNPP ta kafa gwamnati. Ba sai na gaya muku yayi alaƙar waɗannan ƴan gida ɗaya masu kama ɗayan yake da Madugun masu mulki na Jihar Kano ba.
A yau Maigirma Maigirma Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana Kwamishinoni da zasu taya shi Jagorancin al'umar Jihar Kano su sha tara, inda yaga dacewa da ƙwarewar ɗan uwan tsohon Kwamishinan Ma'aikatar Nasiru Sule Garo, ya damƙa masa Ma'aikatar. Wataƙila hakan bai rasa nasaba da cewa ƴan gidan ɗayan sun fi Cancanta a duk faɗin Jihar Kano saboda an mayar da sha'anin mulki gado da mai-mai ta sigogi daban daban.
Yanzu mu ƙaddara Gwamnati mai ci tayi zargin cewa anyi amfani da Ma'aikatar Ƙananan Hukumomi wajen tafka sata da sama da faɗi da dukiyar al'uma. Abun tambayar anan shine idan an tafka wannan badaƙalar wai zai binciki wani?
Mu daina yarda ana wasa da ƙwaƙwalen mu. Mai hankali ya hankalta, mai ganewa ya gane, musamman ƴan siyasar mu da matasa masu tada jijiyar wuya akan sai wane sai wane. Mu sani waɗannan mutanen ba ta mu suke yi ba, buƙatun su da ƙarfafa alaƙar dake tsakanin su shine almuhim a wajen su.
Sun fi son kansu da ci gaban Jihar Kano da al'umar ta, kuma a shirye suke su cigaba ɓullo da sabbin dabaru na gwara kan al'uma domin su samu damar cigaba da cin karensu ba yanka balle babbaka.
A kwanan nan duk da irin sukar da Maigirma Gwamna mai ci yayi ta yiwa tsohon Gwamna Ganduje na shigo da Iyalan sa a sha'anin mulki ya baiwa ɗan sa wato ɗan Yayansa hukuma sukutum don ya Jagoran ta.
Don haka idan kuna tunanin Kwankwaso ko Ganduje zai fifita buƙatar ka akan na kusa da shi, to ku sake tunani.
Wataƙila Yaƙi sai da Kwamanda mai ƙwarewa kuma jarumta na iya bin zuri'a.
Na barku lafiya... Kun ga tafiyata 🚶🚶🚶
Sai kun saki jina.
Naku mai ƙoƙarin tuna muku abinda kuka manta Malam Mai Ɓarota
Comments
Post a Comment