KIRA DON YIN GASKIYA DA ADALCI GA HON. ALHASSAN ADO DOGUWA

Bankaɗo Siyasar Ramukon Gayya da Yaƙi da Ƴan Adawa: Cin Zarafin Hon. Alhassan Ado Doguwa da Gwamnatin Jihar Kano Ke Yi - Haruna Abubakar Bebeji

Gabatarwa:
A ƴan kwanakin nan dai siyasar Najeriya, musamman anan Jihar Kano tana ta fama da cin zarafi da dama da ake yi wa ‘ƴan adawa. Ɗaya daga cikin irin wannan lamari dake tada hankalin al'uma shine yadda ake ci gaba da Zaluntar Sardaunan Rano, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ɗan siyasa mai ƙwazo da mutunci a matakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa.  Wannan hari mara tushe da ake kai masa da cin zarafi da taɓa mutuntakar sa da gwamnati mai ci ke yi na haifar da babbar tambaya kan yanayin dimokraɗiyya da adalci a cikin al'ummarmu.

Nasarorin Hon. Alhassan Ado Doguwa:
Hon.  Alhassan Ado Doguwa, fitaccen ɗan majalisar wakilai na Majalisar Ƙasa ta 10, ya kasance yana cigaba da nuna bajintarsa  ga al’ummar mazaɓarsa da kuma al’ummar Najeriya. Wakilin na mazaɓar Majalisar Tarayya na Tudun Wada/Doguwa, ya tabbatar da kansa a matsayin ƙwararren ɗan majalisa wanda aikinsa ya wuce aiki na siyasa.  Nasarorinsa na ban mamaki da sadaukar da kai ga al'ummarsa ba shakka sun sanya shi a cikin zuƙatan al'ummar mazabarsa.
Tarihin Zantuka Marasa Tushe:
Yana da kyau a lura cewa a baya dai an wanke Hon. Alhassan Ado Doguwa daga dukkan tuhume-tuhumen da gwamnatin jihar Kano ta yi masa, a ƙarƙashin gwamnatin Maigirma Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Waɗannan tuhume-tuhumen sun haɗa da tada husuma, kisan kai, da kuma haddasa mummunar illa ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a lokacin babban zaɓen ƙasa.  Ya kamata a ce tsari da matakin shari'a da aka bi a waccan lokuta, wanda ya same shi ba shi da wani laifi, ya kawo ƙarshen waɗannan zarge-zarge. Sai dai kuma kash! Gwamna mai ci Abba Yusuf na neman sake gabatar da shi tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya bisa waɗannan tuhume-tuhumen da aka riga aka wanke shi, waɗanda ke da alaƙa da wani abu mai kama da cin zarafi na siyasa.

Amfani da Bambanci na Siyasa wajen Zaluntar sa:
A yanzu dai ta tabbata cewa salon da Gwamnatin NNPP a jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta ɗauka na zalunci da cin zarafin Hon.  Alhassan Ado Doguwa ba wani abu sai banbancin dake tsakanin su na siyasa ko Jam'iyya, wanda suke amfani da wasu dabaru marasa kan gado da a tunanin su za su iya rufe shi ko kuma karya lagon sa da rage masa tasiri a siyasance. A matsayinsa na ɗan Jam'iyyar adawa da al’ummar mazaɓarsa ke so kuma suke mutunta shi, kafuwar sa da ƙarfin siyasar da yake da shi a yankin sa, barazana ce ga jam’iyya mai mulki a jihar Kano. Wannan salon cin zarafin sa domin ɓata masa suna da suka ɗauko, ba komai ba ne face ƙoƙarin raunana sunansa da mutuncin sa da ya gina a tsawon shekaru da ya ɗauka yana sadaukar da kansa wajen hidimtawa al'umar sa.

Barazana Ga Dimokuraɗiyya da Adalci:
Zaluntar ƴan Jam'iyyar adawa ba wai hari ne ga dimokuraɗiyya kaɗai ba, hakan babban cin zarafi ne ga ƙa'idojin adalci.  Irin waɗannan munanan ayyukan da suke yi, suna yi ne don su aika saƙo mai ban tsoro ga waɗanda suke ƙalubalantar su, da nufin daƙile muryoyin ƴan adawa da sanyaya musu gwiwa don kada su samu ƙalubale. Hakan wani al’amari ne mai matuƙar tayar da hankali wanda ke sanya ayar tambaya akan ingancin tsarin siyasarmu.
 
Kiran Yin Daidai da Adalci:
A matsayinmu na ƴan kasa nagari da masu fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya, ya zama wajibi a gare mu mu tsaya tsayin daka wajen yaƙar duk wata fitinar siyasa da ke barazana ga tsarin al’ummarmu.  Yunƙurin gwamnati mai ci na ɓata sunan Hon. Alhassan Ado Doguwa dole ne ya fuskanci turjiya tare da neman an yi gaskiya da adalci.

Rufewa:
A ƙarshe, Hon. Alhassan Ado Doguwa a matsayin sa na jajirtaccen Wakilin al'uma da musu hidima, yana da kyau masu yaƙi da shi irin na siyasa, ɗamarar da suka ɗaura na ganin sun kai shi ƙasa na zai taɓa tasiri a kansa ko taɓa mutuntakar sa ba, kuma abubuwan da suke yi da mugun nufin da suke ƙullawa a kansa ba zai rusa shi kamar yadda suke rushe gine-gine ba bisa ƙa'ida ba ta hanyar zargin sa da wasu ƙagaggun laifuka marasa tushe na siyasa ba.  Zaluncin da ake yi masa shi yake tabbatar mana da cewa har yanzu dimokuraɗiyyar mu tana da rauni saboda masu neman yin amfani da ita don amfanin kansu da biyan buƙatar su ta siyasa.  Haƙƙi ne da ya rataya a wuyanmu mu yi Allah wadai da irin waɗannan munanan ayyuka da kuma neman adalci da ganin an yi daidai, da kuma komawa kan haƙiƙanin tsarin dimokuraɗiyya a wannan jiha tamu mai albarka da masa ƙasa baki ɗaya.

Sunana Haruna Abubakar Bebeji.

Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya.  Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su. 

Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci.  Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.  

A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina. 

Na gode da ziyartar shafina.

Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.

Comments

Popular posts from this blog

CELEBRATING KANO STATE'S MONUMENTAL ACHIEVEMENTS UNDER GOVERNOR AKY

Northern Nigerian Blackout: An Open Letter to Mr. President and Northern Nigerian Leaders

Celebrating the Clearing of FX Backlogs: An Important Milestone for Nigeria's Economy