JIHAR JIGAWA ZATA SAMU ƊUMBIN ALKHAIRAI LOKACIN GWAMNA NAMADI

Alƙawarin Da Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi Ya Ɗauka na Gyara Tsarin Ma’aikatan Gwamnati Da Rungumar Suka ko Adawa mai Tsafta Abun A Yaba Masa ne – Haruna Abubakar Bebeji

Shahadar Rantsuwa da sabon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi ya karɓa a kwanakin baya, ya haifar da sabon fata ga al’ummar Jihar. Kyakkyawar ƙuduri da niyar da yake da shi wajen inganta ayyukan ma'aikatan jihar da kuma amincewa da suka mai ma'ana, ya nuna cewa Gwamna Namadi ya shirya tsaf domin jagorantar Jigawa zuwa mataki na gaba.  Yunƙurin da ya bayyana zai yi na samar da ababen more rayuwa a jihar na kara ƙarfafa hangen nesansa na samar da makoma mai kyawu ga kowa.

Gwamnan ya ɗauki waɗannan alkawura masu nuni da kyakkyawar yanayi nan gaba ne a liyafar cin abinci da aka shiryawa Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma Sanata Babangida Hussaini, Gwamnan ya jaddada ƙudirin sa na hidimtawa al’ummar Jihar Jigawa baki ɗaya.  Ya kuma jaddada cewa dukkanin shugabanni tun daga kan gwamna da jami'an gwamnatin jiha da kuma ‘yan majalisar tarayya da na jiha za su yi aiki tuƙuru domin cika alƙawuran da suka ɗauka da yiwa al'umar Jihar abinda suke fata.

Alƙawarin da Gwamna Namadi ya yi na sake farfaɗo da tsarin ma’aikatan jihar abin a yaba ne, kuma yana da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantaccen shugabanci a jihar Jigawa. Ta hanyar inganta ayyukan ma'aikatan gwamnati, gwamnati zata samar da ingantattun kayan aiki don isar da ingantattun ayyuka ga al'uma da samar da kyakkyawan yanayi da ya dace da zamani don samar da cigaba mai ɗorewa.
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a jawabin Gwamna Namadi shi ne yadda ya bayyana shirin sa na amincewa da suka mai ma’ana. Wannan tsari na buɗaɗɗiyar zuciya yana nuna ainihin burinsa na inganta al'amuran jama'a da kyautata zamantakewa da bunƙasa tattalin arzikin jihar.  Ta hanyar yin la'akari da ra'ayoyin al'umar Jihar da masu ruwa da tsaki, yana nuna irin shirin da yake da shi na tafiyar da gwamnatin sa akan kyakkyawar turba.

Dangane da alƙawuran da ya ɗauka na samar da ababen more rayuwa kuwa, Gwamna Namadi yana jaddada manufarsa ne na samar da cigaba. Ta hanyar saka hannun jari a ɓangarori masu muhimmanci kamar sufuri, wutar lantarki, ilimi, da kiwon lafiya, jihar zata yi fice kuma ta zamanto zakaran gwajin dafi wajen janyo masu zuba hannun jari, haɓaka tattalin arziki, da inganta rayuwar al'uma.  Irin waɗannan ayyukan samar da ababen more rayuwa babu shakka za su mayar da jihar Jigawa ta zama cibiyar cigaba da yin fice a tsakanin takwarorinta.
A ƙarshe, salon da Gwamna Namadi ya ɗauka wajen tafiyar da gwamnatin sa, kamar yadda alƙawuran da ya ɗauka na inganta tsarin aikin gwamnati da rungumar suka mai ma'ana, ya cancanci a yaba masa.  A yayin da yake jagorantar ƙudurin Gwamnatin jihar Jigawa na samar da cigaba mai ɗorewa, yana da matuƙar muhimmanci ga al'umar Jihar Jigawa su bashi haɗin kai da gwamnatinsa domin samun nasarar da ake buƙata ga kowa. Jagora mai hangen nesa da jajircewa wajen kyautata rayuwar al’ummarsa, muna da kyakkyawar zaton cewa lokacin mulkin Gwamna Namadi zai samar da cigaba mai ɗorewa kuna abin alfahari ga al'umar Jihar Jigawa.

A matsayin sa na mai kishin Jihar Jigawa, ko shakka babu, Gwamna Namadi, yana da burin ɗaukaka jihar Jigawa zuwa wani matsayi mai girma, kuma al'umar Jihar Jigawa na sa ran samun kyakkyawan sauyi a nan gaba.
Sunana Haruna Abubakar Bebeji.

Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya.  Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su. 

Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci.  Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.  

A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina. 

Na gode da ziyartar shafina.

Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa. 

Comments

Popular posts from this blog

CELEBRATING KANO STATE'S MONUMENTAL ACHIEVEMENTS UNDER GOVERNOR AKY

Northern Nigerian Blackout: An Open Letter to Mr. President and Northern Nigerian Leaders

Celebrating the Clearing of FX Backlogs: An Important Milestone for Nigeria's Economy