GALLAZA MANA DA DUHU DA KAMFANIN WUTAN LANTARKI NA KEDCO KEYI BA TARE DA WANI DALILI BA: AL'UMAR JIHOHIN KANO, KATSINA, DA JIGAWA SUNA BUƘATAR ƊOKI

GALLAZA MANA DA DUHU DA KAMFANIN WUTAN LANTARKI NA KEDCO KEYI BA TARE DA WANI DALILI BA: AL'UMAR JIHOHIN KANO, KATSINA, DA JIGAWA SUNA BUƘATAR ƊOKI- Haruna Abubakar Bebeji


Wani abin takaici da muke fama da shi, shine yadda miliyoyin al’ummar jihohin Kano, Katsina da Jigawa suka shiga cikin mawuyacin hali na rayuwa a ƴan kwanakin nan, inda suka shiga cikin wani yanayi maras daɗi sakamakon rashin wutar lantarki da aka shafe kusan kwanaki huɗu ana fama da shi.  Duk da irin zazzafan yanayi da ake fama da shi a yankunan, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) ya kasa sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, ya kasa samar da wutar lantarki a jihohin uku, lamarin da ya jefa jama’a cikin duhu, ƙunci da gurgunta harkokin kasuwanci.  Wannan mummunan yanayi ya yi tasiri sosai ga harkokin kasuwanci, ya kawo cikas ga rayuwar yau da kullum, kuma ya haifar da ɓacin rai a tsakanin mazauna jihohin.

Mawuyacin Halin da Muka Tsinci Kanmu a Ciki

A cikin kwanaki huɗu da suka gabata, waɗannan jahohin sun gamu da ɓacin rai mai yawa kuma abun sai ƙara ta'azzara yake yi. Rashin samun wutar lantarkin ba wai kawai ya haifar da rashin haske ba ne;  ya jefa al'uma cikin wani mummunan yanayi na takura, ya gurgunta harkokin kasuwanci, da kuma jawo wahalhalu masu yawa ga al'ummar da dama ƙalubalen rayuwar yau da kullum ya musu dabaibayi.

Wani abin takaicin ma shi ne, duk da ƙorafe-korafe da mafiya yawa daga mazauna yankunan suke tayi, Kamfanin KEDCO na cigaba da nuna halin rashin ko-in-kula da mawuyacin halin da al'uma suke ciki; babu wata ƙwaƙƙwarar hujjar gazawar su, kuma babu nuna damuwa da  mawuyacin halin da suka jefa mutane a ciki. Wani abin takaici kuma shi ne, maimakon a gaggauta maido da wutar lantarkin, sai suka ƙara dagula al’amura, ta hanyar ci gaba da kawowa mutane takardar neman biyan kuɗin wuta (bill) da basu mora ba, wanda hakan cin fuska ne ga al'umomin yankunan. Waɗannan salon zalincin bai dace a ƙyale ko a ƙyale su ba tare da sun magance su da gaggawa ba.

Allah Wadai da Buƙatun Gaggauta Maidowa Al'uma da Hasken Wutan Lantarki:

Al'ummar jihohin Kano, Katsina da Jigawa ba su cancanci wannan salon zaluncin ba.  Ba zamu zura ido kawai KEDCO ta yi aiki tare da irin wannan gazawar da rashin kulawa ga wahalhalun da abokan cinikinta ke fuskanta ba.  Dole ne ta ɗauki alhakin wannan gazawa tare da bawa abokan hulɗarta haƙuri na wannan gazawa ko rashin ƙwarewa.

Da babban murya, muna Allah wadai da gazawar KEDCO wajen dawo da wutar lantarki, muna kuma kira ga kamfanin da ta gaggauta magance wannan masifa, ta hanyar maido da wutar lantarki a jihohin uku ba tare da ɓata lokaci ba, tare da daina cuzgunawa abokan hulɗarta ta hanyoyin kawo musu takardar biyan kuɗi na son rai.  Rayuwar miliyoyin jama'a na fuskantar ƙalubale da takura, sakamakon wannan rashin wuta.  Daga iyalai da ke fafutuka yadda zasu ci da Iyalan su, zuwa ƴan kasuwa masu gudanar da harkokin kasuwancin su a irin wannan lokaci mai tsanani, sakacin KEDCO ya ƙara ta'azzara lamuran.

A ƙarshe, lokaci ya yi da KEDCO zata gane muhimmanci da girman ayyukanta.  Al’ummar Jihohin Kano, Katsina da Jigawa sun buƙatar a gaggauta maido musu da wutan Lantarki, tare da biyan diyya ko ɗaukewa mutane biyan kuɗin wuta domin saka musu bisa  wahalhalun da aka sha.

Haka kuma, ya zama dole ga kamfanin KEDCO dole tayi dogon nazari da bincike mai tsanani don gano dalilin gazawarta domin goge mummunan fentin da suka shafawa kansu tare da kuma tabbatar da cewa sun kiyaye aukuwar irin wannan yanayi a nan gaba ba.

Haka kuma lokaci ya yi da KEDCO zata yarda da ɗaukar nauyin wannan laifi da suka aikata tare da gaggauta maido da hasken wutan Lantarki a yankunan da abin ya shafa.  Ƴancin cin moriyar samun wutar lantarki wani muhimmin haƙƙi ne na dukkan ƴan Najeriya; don haka bai dace kamfanin na KEDCO ya bar mutanen da abin ya shafa cikin duhu ba tare da wani ƙwaƙƙwarar dalili na da kuma daina cazar ko bin tsarin biyan kudin wutar lantarkin da bai dace ba.

Jama’ar wadannan jihohin, duk da irin juriyarsu, bai kamata a yi sakaci irin wannan ba.  Haƙƙin KEDCO ne ya gyara wannan mummunan yanayi cikin gaggawa tare da maido da haske da sanya nutsuwa da yarda a cikin rayuwar mutanen da suke yiwa hidima. Ya kamata wannan al'amari ya zama wata sila na kawo kyakkyawar sauyi, inda zasu fifita buƙatu da jin daɗin jama'a, domin a yanayin da muke ciki yanzu, samar da wutar lantarki ba alfarma ba ce, hidima ce mai muhimmanci da ya kamata a samar cikin inganci da kulawa.


Sunana Haruna Abubakar Bebeji.

Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya.  Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su.

Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci.  Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.  

A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina.

Na gode da ziyartar shafina.

Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.


Comments

Popular posts from this blog

JUSTICE SERVED: TRUTH PREVAILS AS RAHAMA SAIDU'S TIKTOK CLAIMS DEBUNKED

SANUSI BATURE, AN ACCIDENTAL SPOKESMAN: THE REJOINDRER

#TheAliPateEffect - A Milestone for Maternal Health in Nigeria