BARKA DA SALLAH

Masu Karatu da Masu Bibiyan Shafina,

Yayin da muke bikin Babbar Sallah, ina so in yi amfani da wannan dama don mika gaisuwa ta gareka.  Ina fatan wannan babban rana zai samar da farin ciki da albarka ga rayuwarku.

Eid-el-Adha, wanda kuma aka fi sani da idin layya, lokaci ne da iyalai suke taruwa domin tunawa da yadda Annabi Ibrahim ya ƙuduri aniyar sadaukar da ɗansa Ismail domin biyayya ga Allah SWT. Lokaci ne na tuna baya, godiya, da haɗin kai tsakanin al'ummar musulmi.

A wannan lokacin, mu tuna muhimmancin sadaukarwa da muhimmancin wannan lokaci.  Mu tuna da kyawawan halayen son juna da tausayi da ya kamata mu nuna ga wasu.  Yayin da muke taruwa tare da masoyanmu, muma mu nuna halayen karimci ga mabukata, tare da rungumar darasin da Idin Layya ya koyar da mu.

A irin wannan lokaci da muke sadaukar da abun da Allah Ya bamu domin layya, mu yi ƙoƙari mu sanar da farin ciki da kawo canji mai kyau a rayuwar wasu.  Mu taimakawa masu karamin karfi, mu agazawa marasa galihu, mu yaɗa alheri da soyayya a junan mu.

Ina kuma amfani da wannan dama wajen miƙa godiyata ga duk masu bibiyar shafina na penbebeji.blogspot.com. Bibiyata da haɗin kai da kuke bani suna taimaka mini matuƙa wajen cigaba na, kuma ina godiya da irin goyon baya da ƙarfafa mini gwiwa da kake yi.

Yayin da muke cigaba da bukukuwan babbar Sallah, muyi amfani da damar da muka samu domin bawa Iyalan mu lokacin su da sada zumunci ga ƴan uwan mu da abokan arzikin mu da masu ƙaunar mu.  Mu kuma yi amfani wannan lokaci domin tuna irin  ni'imomin da Allah Ya mana, mu yi addu'o'in samun zaman lafiya, wadata, da yalwar arziki ga kowa.

Da fatan dukkanin ku da iyalanku zaku cigaba da bukukuwar babban Sallah cike da farin ciki, da annashuwa.

Barkan mu da Sallah, Allah Ya maimaita mana, Amin!

Haruna Abubakar Bebeji
penbebeji.blogspot.com

Comments

Popular posts from this blog

CELEBRATING KANO STATE'S MONUMENTAL ACHIEVEMENTS UNDER GOVERNOR AKY

MUHAMMADU SANUSI II'S BETRAYAL OF PEOPLE'S TRUST

JUSTICE SERVED: TRUTH PREVAILS AS RAHAMA SAIDU'S TIKTOK CLAIMS DEBUNKED