Ayi taka-tsantsan dangane da Rusau: Bai kamata Rusau Yasa a ƙara asarar rayuka a Jihar Kano ba
AYI TAKA-TSANTSAN DANGANE DA RUSAU: BAI KAMATA RUSAU YASA A ƘARA ASARAR RAYUKA A JIHAR KANO BA – Haruna Abubakar Bebeji.
Ayyukan Rusau da Maigirma Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya ɗauko a ƴan kwanakin nan, domin kamar yadda yace don gyara yadda aka raba kadarorin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba ga makusanta da muƙarraban tsohon Gwamna Ganduje, ya haifar da munanan al’amura. Rushe-rushen ya haifar da ruɗani da ɓarna a jihar. Waɗannan rusau da yake tayi, yayin da ake ƙoƙarin tabbatar da bin doka da oda kamar yadda ya ce, ya samar da wata kafa ga wasu ɓata gari inda suke cin karensu ba babbaka wajen lalata da kwashe kayan da aka rushe. Duk da cewa matakin kamar yadda yake cewa, an yi shi ne domin a dakatar da bayar da kadarorin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, shima Maigirma Gwamnan ba tare da bin ƙa’ida ba, ya gaza yin tunani yadda ya kamata a kan illar ayyukansa.
Abin takaici, wannan ya haifar da asarar rayuka ga wasu daga cikin waɗannan mutane. Yana da matuƙar muhimmanci a magance wannan lamari mai cike da baƙin ciki tare da yin kira ga Gwamna Abba Yusuf da ya dakatar da cigaba da rusa wurare kafin a yi asarar rayukan da ba su ji ba, basu gani ba.
Da yawa daga cikin gine-ginen da aka rusa, waɗannan ɓata gari suna amfani da damar da suka samu wajen yi awon gaba da sace kayayyaki da kayan aiki daga cikin gine-ginen. Hakan dai na nuni da cewa matakin da gwamnan ya ɗauka ba wai ya janyo hasarar dukiya ne kaɗai ba har ma da asarar rayuka.
Kwanan nan ne wasu ɓata gari suka maƙale ko ace gini ya rufto musu a ginin otal din Daula da aka rusa, lamarin da ya sa wasu daga cikinsu suka rasa rayukansu. Wannan lamari ne mai ban tausayi da bai kamata ya faru ba idan da a ce gwamnan tayi taka-tsantsan wajen gudanar da ayyukanta.
Abinda ya kamata ayi maimakon Rusau
Ƙudirin da Gwamna Abba Kabir Yusuf yace na gyara kura-kurai da aka aikata a baya, idan anyi shi da kyakkyawar manufa abin a yaba ne, amma ya kamata ayi nazarin abinda ka iya biyo baya a yayin aikin rushe-rushen. Rusau ba zai magance wannan matsalar ba, a maimakon haka, ƙwacewa da sake dawo da waɗannan kadarorin zai sa su zama sun fi amfani ga jama’a, ba tare da yin kasada da aikata wani ɓarnar asarar rayuka ba.
A matsayinmu na ƴan ƙasa masu kishin ƙasa, yana da kyau mu yi kira ga gwamna da ya kawo ƙarshen wannan rusau ɗin. Rusau ba mafita bace ga matsalar da ake fuskanta. A maimakon haka, ya kamata gwamnati ta ƙwace waɗannan kadarorin maimakon lalata su don kawai a ba wa ƴan iska damar yin sata da ɓarnata dukiyoyin al'uma.
Abinda Rusau Ya Haifar
Al’amarin da ya faru a ranar Alhamis da ta gabata, inda gungun wasu matasa da suke yunƙurin satar kayayyaki da kayan aiki daga ginin otal din Daula da aka ruguje, gine ya rufto musu ya kuma danne su har ya kai da rasa rayukan wasu, ya nuna illolin da ke tattare da rushewar da ake yi ba tare da nazari ba. Waɗannan mummunan abinda ya auku, za'a iya kauce masa inda anbi wasu ƙa'idoji da suka dace. Dole ne Gwamna Abba Yusuf ya ɗauki alhakin rayukan da suka salwanta tare da ɗaukar matakin gaggawa don hana afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.
Dole Maigirma Gwamna ya ɗauki alhakin wannan aikin da ya bada umarni ayi. Idan bai hana wannan rusau ɗin ba, za a ci gaba da asarar rayuka da dama, sannan kuma haƙƙin jinin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ne zai cigaba da dabaibaye hannun Maigirma Gwamnan.
Kiyaye Rayuwa Yayin Neman Adalci
Babu wanda zai musanta cewa dole ne a gyara yadda ake raba kadarorin gwamnati ba bisa ka'ida ba, amma yana da matuƙar muhimmanci a kiyaye rayukan mutane yayin aikin. Maimakon rushe gine-ginen gaba ɗaya, ya kamata Gwamna ya binciko wasu hanyoyin magance wannan matsala. Ya kamata ya yi la'akari da aiwatar da wani tsari na bincike da kuma gurfanar da masu laifi a gaban kotu, ba tare da jefa rayukan marasa laifi cikin haɗari ba.
Lokaci ya yi da Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sake duba tsarin yadda yake gudanar da ayyukansa, ya kuma sa maslahar al’umma a gaba. A matsayinsa na jagora, ya zama wajibi ya tabbatar da cewa ayyukansa ba su yi illa ga al'umar Jihar Kano ba, da ba su ji ba ba su gani ba. Don haka muna kira gare shi da ya gaggauta dakatar da waɗannan ruguje gine-gine tare da samar da ingantacciyar hanyar magance matsalar da ake fama da ita.
Tsawatarwa daga Majalisar Dokoki da Dakatar da rusau
Ya kamata Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta shiga tsakani ta kuma baiwa gwamnan ƙwarin guiwa ya sake duba dabarun mulkin sa. Ta hanyar dakatar da rusau, hukumomi na iya daƙile asarar rayuka da basu ji ba, ba su gani ba, tare da bada damar yin garambawul. Za a iya amfani da kadarorin da aka ƙwace a danƙawa Hukumar Zuba Jari da Kula da Kadarorin Gwamnati (KSIP) ko ayi amfani da su domin amfanin jama’a, walau makarantu, asibitoci, ko cibiyoyin al’umma da za su amfanar da al’ummar Jihar Kano.
Bugu da ƙari, yana da mahimmanci a magance matsalar yara ɓata gari da ke cin gajiyar waɗannan rusau. Ya kamata gwamnati ta tura isassun jami’an tsaro domin daƙile duk wani abu na ɓarna ko sata a lokacin da ake shirin ƙwace waɗannan gine-gine, tare da tabbatar da tsaron kadarorin gwamnati da na masu zaman kansu.
Kammalawa
Yunƙurin da Gwamna Abba Yusuf yake yi na gyara kura-kuran da aka yi a baya wajen rabon kadarorin gwamnati abu ne da wasu ke yabawa. Duk da haka, bai kamata a yi watsi da sakamakon da ba a zata ba na rushewar ginin. Asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba sakamakon ayyukan ɓata gari a lokacin waɗannan rusau lamari ne mai ban takaici da ya kamata a yi gaggawar magance su. Ya zama wajibi Gwamnan ya sake duba tsarinsa tare da mayar da hankali kan wasu hanyoyin da za su kare rayuka tare da tabbatar da adalci. Dakatar da rusau da kuma jagorantar yunƙurin rabon kadarorin da aka dawo da su don amfanin jama'a zai samar da mafita mai ma'ana ga wannan al'amari mai sarƙaƙiya. Ta haka ne kawai za mu iya hana sake zubar da jini, tare da samar da gwamnati mai adalci ga al’ummar Jihar Kano.
Sunana Haruna Abubakar Bebeji.
Ni marubuci ne, mai ƙirƙirar labarai, kuma mai rubuce-rubuce a yanar gizo daga Kano, Najeriya. Na fara rubuce-rubuce ne akan batutuwa da suka shafi siyasa, shugabanci da al'amuran yau da kullun don bayyana ra'ayoyina a kafa irin wannan. Tafi-tafi, rubuce-rubuce na ya zama wata kafa a gare ni don zaburaswa, ƙarfafawa jama'a gwiwa da kuma a wani lokacin nishaɗantar da su.
Na himmatu wajen kawo muku batutuwa masu nishaɗantarwa masu inganci, wanda zai taimaka sannu a hankali wajen inganta rayuwar al'uma. Ina da sha'awar bincike akan sabbin batutuwa, nazari akan harkokin kasuwanci, da muhawara akan abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa da sha’anin mulki ko Shugabanci. Na kan yi rubutu da Turanci ko da Hausa kuma a matsayina na ƙwararren Mai fassara da Tanbihi da yake da shaidar ƙwarewa a waɗannan fannoni a Duniya, na kan yi Fassara daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci.
A sanda da ba na rubutu, ko ƙirƙirar labarai, za ku iya samuna a wuraren da ke da kyakkyawar yanayi ina karatu, ko ina bawa iyalai, ƴan uwa da abokai na lokacina.
Na gode da ziyartar shafina.
Ina fatan zaku dawo don karanta rubuce-rubuce na masu ƙayatarwa.
Comments
Post a Comment