Shirin Yin Aiki (Tiyata) Kyauta ga Mata Masu Juna Biyu (CS) Yayin Haihuwa: Tsari Mai Matuƙar Mahimmanci ga Lafiyar Mata a Najeriya
#TasirinAliPate - Yabawa Farfesa Muhammad Ali Pate na Ƙaddamar da Sabon Shirin Yin Aiki (Tiyata) Kyauta ga Mata Masu Juna Biyu (CS) Yayin Haihuwa: Tsari Mai Matuƙar Mahimmanci ga Lafiyar Mata a Najeriya - Haruna Abubakar Bebeji A wani gagarumin ci gaba na inganta kiwon lafiyar mata masu juna biyu a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa a yanzu za a fara yiwa mata masu juna biyu aikin tiyata (CS) kyauta a yayin haihuwa da buƙatar hakan ta taso ko matan da ke buƙata. Wannan sabon shiri da Babban Ministan lafiya da walwalar jama'a na Tarayyar Najeriya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya jagoranta, ya zo a matsayin wani babban hoɓɓasa da tabbatar da jajircewar gwamnati na rage yawan mace-macen mata masu juna biyu a wajen haihuwa a ƙasar nan. Bayanin da Farfesa Pate ya yi kwanan nan ya jaddada hangen nesa dake ƙunshe a cikin manufofin kiwon lafiya, dake cikin Jadawalin Manufofin Sabuwar Fata wanda aka fi sani da "RENEWED HOPE" na Shugaba Bola Ahmad Tinubu....